News
KANO: One Kano Agenda Ta Yabawa Gwamnan Abba Kabir Kan Zaɓen Murtala Sule Garo A Matsayin Mataimakinsa
Kungiyar One Kano Agenda ta yabawa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, bisa naɗin Murtala Sule Garo a matsayin Mataimakin Gwamna, tana mai cewa matakin na nuna hangen nesa da ƙudurin inganta shugabanci.
A cikin wata sanarwa da Darakta Janar na ƙungiyar, Abbas Abdullahi Yakasai, ya fitar a ranar Laraba, ya ce naɗin wani tsari ne mai muhimmanci da zai taimaka wajen haɗa manufofin gwamnati da bukatun al’umma, musamman a matakin ƙasa.
Kungiyar NDWG Ta Nuna Goyon Baya Kan Naɗin Murtala Garo A Matsayin Mataimakin Gwamnan Kano
Ƙungiyar ta bayyana cewa matakin gwamnan ya nuna fahimta kan buƙatun shugabanci a wannan lokaci, tana mai jaddada cewa irin wannan matsayi na buƙatar ƙwarewa, aminci da kusanci da jama’a.
Ta ƙara da cewa tarihin Garo a harkokin siyasa da ayyukan gwamnati ya sanya shi cikin sahun waɗanda za su taimaka wajen aiwatar da manufofin ci gaban jihar da kuma inganta tsarin mulki.
One Kano Agenda ta kuma yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki su mara wa wannan naɗi baya, ba tare da la’akari da bambancin siyasa ba, tana mai cewa haɗin kai shi ne ginshiƙin samun ci gaba mai ɗorewa.
A ƙarshe, ƙungiyar ta sake jaddada goyon bayanta ga gwamnatin Kano, tare da bayyana ƙwarin gwiwarta cewa wannan naɗi zai taimaka wajen ƙarfafa shugabanci da cimma manufofin ci gaban jihar.
