News
Ranar Ma’aikata: “Muna Cikin Matsin Rayuwa” — Ma’aikatan Najeriya
Yayin da duniya ke gudanar da bikin Ranar Ma’aikata a yau, ɗaya ga watan Mayu, ma’aikatan Najeriya na bayyana ƙuncin rayuwar da suke fuskanta, sakamakon matsin tattalin arziki da ya ta’azzara a ƙasar.
Ranar Ma’aikata rana ce da aka ware a duniya don tunawa da gudummawar ma’aikata da kuma waiwayar nasarori da kalubalen da suke fuskanta. A Najeriya, wannan rana ta zo ne a daidai lokacin da ƙasar ke fuskantar matsi, musamman tun bayan cire tallafin man fetur da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanar da shi a jawabinsa na farko bayan rantsuwa a ranar 29 ga Mayu, 2023. Wannan mataki ya haifar da hauhawar farashin kayayyaki da kuma tashin gwauron zabi na rayuwa.
Lokaci Ya Yi Da Shamsudeen Bala Mohammed Zai Nemi Kujerar Sanata
Ma’aikata da dama sun koka kan yadda mafi ƙarancin albashi na yanzu ba ya wadatar da su wajen biyan buƙatun yau da kullum.
Rahotanni sun nuna cewa har yanzu jihohi 20 daga cikin 36 ba su fara aiwatar da sabon tsarin mafi ƙarancin albashi na Naira 70,000 ba, duk da cewa shugaban ƙasa ya rattaba hannu kan dokar biyan sabon albashin tun ranar 29 ga Yuli, 2024.
Wata ma’aikaciyar gwamnati ta bayyana fatan su da cewa: “Muna fatan gwamnati za ta ƙara albashi. Idan an ƙara, zai sauƙaƙa mana rayuwa, musamman a irin wannan lokaci da komai ya yi tsada.”
Wata kuma ta kara da cewa: “Rayuwa ta yi tsanani, musamman ga mata. Yawanci muna tafiya a kafa saboda kudin mota ya fi ƙarfinmu — inda ake zuwa da Naira 50 yanzu sai da Naira 350. Ga kuma tsadar abinci da sauran abubuwan yau da kullum.”
Ƙungiyoyin ƙwadago sun sha gudanar da zanga-zanga don nuna damuwa kan irin halin da ma’aikata ke ciki, tare da kiraye-kirayen da gwamnati ta dauki matakan rage musu wahala. Sai dai har yanzu, ‘yan ƙwadago na cewa ba a ga wani sauyi na a-zo-a-gani ba daga bangaren gwamnati.
Ranar ta bana, sabanin murna da shagulgula, ta kasance rana ta tunani da ƙorafi ga dimbin ma’aikatan Najeriya.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News3 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
