Opinion
Lokaci Ya Yi Da Shamsudeen Bala Mohammed Zai Nemi Kujerar Sanata

Shamsudeen Bala Mohammed, wanda aka fi sani da Dangaladiman Duguri, na kara jan hankalin jama’a a siyasar Bauchi, musamman ma a yankin Bauchi ta Kudu. Shi ɗan Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, kuma injiniya ne a fannin jiragen sama. Duk da haka, bai tsaya gefe ba wajen kallon siyasar mahaifinsa, sai da ya shiga ciki da kansa domin tallafa masa da kuma al’ummar jihar.
Wani mai fashin baki da ke kusa da tafiyar siyasar jihar ya bayyana cewa sun fara hulɗa da Shamsudeen ne kafin mahaifinsa ya zama gwamna. “Ko da ban taɓa haɗuwa da shi kai tsaye ba, ya haɗa ni da mahaifinsa, wanda hakan ya zama tushe na wata dangantaka mai amfani,” in ji shi.
Majalisar Shari’ar Musulunci Ta Naɗa Sheikh Bashir Aliyu Umar A Matsayin Sabon Shugaba
Shamsudeen ya shahara da jajircewarsa wajen karfafa matasa a harkokin siyasa. A cewar wasu, yana da buri da kuma kishin al’umma, duk da cewa wasu na da sabani da wasu hanyoyin siyasar sa. Amma abin da ba za a iya karyatawa ba shi ne cewa yana da saukin kai, karimci, da son ganin al’umma na ci gaba.
“Shamsu ba wai kawai ya dogara da matsayin da mahaifinsa ke kai ba ne. Ya fito fili yana ba da gudunmawa domin ganin gwamnatin Kaura ta kafa tubalin ci gaba mai dorewa,” in ji wani matashi daga yankin Bauchi ta Kudu.
A matsayin sa na matashi da ya dade yana fafutukar ganin matasa sun samu wakilci a siyasa tun 2015, da dama na ganin cewa lokaci ya yi da Shamsu zai nemi kujerar Sanata domin wakiltar Bauchi ta Kudu. Wasu na ganin zai iya taka rawar gani kamar yadda Bello El-Rufai ke yi a Majalisar Wakilai.
Shamsudeen dai yana da farin jini tsakanin matasa, kuma ana masa kallon wani gwarzon matashi da zai iya kawo sauyi a wakilcin Bauchi.
Gaba dai, gaba dai, Dangaladiman Duguri!
Adnan Mukhtar
Mai Sharhi Kan Al’amuran Siyasa kuma Malamin Jami’a.