News
Hadakar Malamai Sun Bukaci A Gudanar Da Siyasar Kano Cikin Lumana
Hadakar Malamai da Kungiyoyin Musulunci a Jihar Kano ta bukaci ’yan siyasa da magoya bayansu da su guji kalaman tunzura jama’a tare da gudanar da harkokin siyasa cikin lumana domin tabbatar da zaman lafiya a jihar.
A cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar, ta nuna damuwa kan yadda ake ci gaba da samun zafafan kalamai da wasu dabi’u da ka iya haddasa tashin hankali a tsakanin masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa.
Jami’an NDLEA Sun Bankaɗo Wasu Koguna Da Ake Hada-hadar Miyagun Ƙwayoyi A Kano
Kungiyar ta ce siyasa bai kamata ta zama wata hanya ta haifar da rikici ko rarrabuwar kawuna a tsakanin al’umma ba, illa ta kasance wata kafa ta gabatar da manufofi da shirye-shiryen ci gaba.
Har ila yau, hadakar ta yi kira ga matasa da kada su bari a yi amfani da su wajen tayar da zaune tsaye ko aikata ayyukan da za su iya kawo barazana ga zaman lafiya da tsaron jama’a.
Sanarwar ta kara da cewa Kano na da tarihin zaman lafiya da mutunta juna, don haka akwai bukatar dukkan bangarori su hada hannu wajen tabbatar da dorewar wannan yanayi.
Kungiyar ta kuma yaba da kokarin hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki wajen tabbatar da zaman lafiya a jihar.
Sanarwar dai na dauke da sa hannun sakataren kungiyar, Dakta Sa’idu Ahmad Dukawa.
