News
Burkina Faso ta Dakatar Da Ƙungiyoyi Masu Zaman Kansu Sama Da 200
Shugaban ƙasar Burkina Faso ya ba da umarnin soke kimanin ƙungiyoyi masu zaman kansu 200.
A jumlace zuwa yanzu ƙasar ta yankin Sahel ta dakatar da ƙungiyoyi masu zaman kansu 205, inda dukkansu ke cikin Burkina Faso, kuma suke aiki a fannonin lafiya da ilimi da ‘yancin mata da noma da muhalli da al’adu da kuma wasanni.
Jami’an NDLEA Sun Bankaɗo Wasu Koguna Da Ake Hada-hadar Miyagun Ƙwayoyi A Kano
A watan Yulin shekarar 2025, shugaban ƙasa Kyaftin Ibrahim Traore ya rattaba hannu kan wata doka da ta taƙaice ayyukan ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama da kuma wasu ƙungiyoyi.
“A lokacin dakatarwar, ayyukan da ke nuna cewa ƙungiyoyin na biyayya ga doka ne kawai aka ba su damar yi,” in ji dokar ta gwamnati.
Burkina Faso tana yawan zargin ƙungiyoyi na ƙasa da ƙasa masu zaman kansu da kuma ƙungiyoyin ba da agaji da ke samun tallafi daga ƙetare kan leƙen asiri ko kuma haɗa baki da ‘yanta’adda da ke yaƙar sojin ƙasar.
