Connect with us

Politics

Bichi Ya Ayyana Aniyarsa Ta Tsayawa Takarar Sanatan Kano Ta Arewa A Jam’iyyar APC 

Published

on

IMG 20260506 WA0010

Tsohon ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Bichi, Hon. Mahmoud Baba Bichi, ya ayyana aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar Sanatan Kano Ta Arewa a zaɓen 2027 karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

‎Bichi ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai ziyara sakatariyar jam’iyyar APC ta Jihar Kano, inda ya ce ya zo ne domin sanar da shugabannin jam’iyyar kudirinsa na neman kujerar majalisar dattawa.

Advertisement

IGP Disu Ya Kafa Sabuwar Rundunar Musamman Don Yaƙi Da Manyan Laifuka

‎Ya bayyana cewa tuni ya sayi fom ɗin tsayawa takara a hedikwatar APC ta ƙasa da ke Abuja, domin bin ƙa’idojin zaɓe da aka shimfiɗa. Ya ƙara da cewa, duk da cewa ya kamata ya sanar da shugabannin jiha tun da wuri, ƙarancin lokacin da aka bayar ne ya sa ya fara kammala wannan tsari a matakin ƙasa.

Advertisement

‎Bichi ya jaddada cikakken biyayyarsa ga jam’iyyar APC, yana mai cewa burinsa na siyasa yana cikin jam’iyyar, kuma yana fatan samun goyon bayan shugabanni da mambobinta.

‎Tsohon ɗan majalisar ya kuma buƙaci shugabannin jam’iyyar da su yi la’akari da batun daidaito wajen rabon dama, yana mai cewa ƙananan hukumomin Bichi, Dawakin Tofa da Dambatta ba su taɓa samar da sanata ba tun bayan dawowar mulkin dimokuraɗiyya a shekarar 1999.

Advertisement

‎A cewarsa, lokaci ya yi da jam’iyyar za ta duba yiwuwar bai wa wasu ƙananan hukumomi dama su fito da ɗan takara, maimakon ci gaba da fitowa daga Karamar Hukumar Kabo kaɗai.

‎Da yake mayar da martani, Sakataren APC na Jihar Kano, Farfesa Yusuf Muhammad Sabo, wanda ya wakilci Shugaban jam’iyyar na jiha, Hon. Umar Haruna Doguwa, ya yaba wa Bichi kan yadda ya sanar da jam’iyyar aniyarsa cikin tsari.

Advertisement

‎Ya kuma tabbatar da cewa jam’iyyar za ta yi adalci ga duk masu neman takara, tare da tabbatar da bin ƙa’idoji da gaskiya a yayin zaben fidda gwani.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending