Connect with us

Politics

Ibrahim Ali Amin Little Ya Sayi Fom Din Takarar Gwamna A Jam’iyyar ADC

Published

on

IMG 20260507 202912 587

Wani jigo a jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Alhaji Ibrahim Ali Amin Little, ya sayi fom din neman takarar gwamnan Jihar Kano a karkashin jam’iyyar domin tunkarar babban zaben shekarar 2027.

Little ya sayi fom din ne a hedikwatar jam’iyyar ta kasa da ke Abuja, inda ya bayyana kudirinsa na neman jagorancin jihar Kano.

Advertisement

Babu Hujjar Alaƙanta Gwamnati Da Kisan Da Akayi a Kano — Kungiyar NDWG

Da yake jawabi ga manema labarai bayan karbar fom din, tsohon shugaban jam’iyyar APP a Kano ya bayyana cewa yana da yakinin samun nasara a zaben fidda gwani na jam’iyyar da kuma babban zaben shekarar 2027.

Advertisement

Ya ce shiga takarar da ya yi na da nufin samar da ingantaccen shugabanci tare da ciyar da Kano gaba ta fuskar ci gaban tattalin arziki da walwalar al’umma.

A cewarsa, idan aka ba shi dama, zai mayar da hankali wajen yaki da daba da rikice-rikicen siyasa, rage radadin talauci da kuma samar da muhimman abubuwan more rayuwa ga al’umma.

Advertisement

“Abin da ya fi daukar hankalina shi ne rayuwar al’ummar Kano. Za mu tabbatar da samar da ingantaccen ilimi, asibitoci masu kyau, wadataccen ruwan sha da kuma shirye-shiryen tallafa wa marasa karfi,” in ji shi.

Little ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa za ta ba da fifiko ga bunkasa harkar noma, samar da ayyukan yi ga matasa da kuma farfado da masana’antun Kano domin habaka tattalin arzikin jihar.

Advertisement

Ya kara da cewa akwai bukatar dawo da Kano matsayinta na cibiyar kasuwanci a Arewacin Najeriya ta hanyar samar da yanayi mai kyau ga masu zuba jari da bunkasa masana’antu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending