News
JAMB Ta Sanya Ranar Da Za A Fara Jarabawar UTME Ta 2026
Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta Nijeriya (JAMB) ta sanar da fara fitar da takardun bayanin zama jarabawar UTME ta shekarar 2026 ga ɗaliban da suka yi rajista.
A cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Fabian Benjamin, ya fitar a Abuja ranar Alhamis, ya bayyana cewa ɗalibai yanzu za su iya cire takardunsu (slip) ta shafin yanar gizon hukumar domin sanin cikakken bayani kan jarabawarsu.
TAFTA Ta Horar da Matasa 28,000 A Kano, Ta Samar da Aikin Yi Ga 16,000
Sanarwar ta ƙara da cewa za a fara gudanar da jarabawar ne daga ranar 16 ga watan Afrilu, inda aka buƙaci ɗalibai su duba ranakun da aka tsara musu, wuraren da za su rubuta, da kuma lokacin da za su halarta.
Hukumar ta shawarci ɗalibai da su hanzarta cire takardunsu tun da wuri, tare da tabbatar da sun san cibiyoyin da aka ware musu kafin ranar jarabawa, domin kauce wa duk wata tangarda.
Ta kuma bayyana cewa an tsara wa kowane ɗalibi jadawalin jarabawa na musamman, tare da umarnin su isa cibiyoyin jarabawar da wuri domin kammala tantancewa kafin fara jarabawar.
A bangaren tsaro, JAMB ta ce ta ƙara ɗaukar matakan sa ido a bana domin dakile duk wani yunkuri na magudin jarabawa.
Haka zalika, hukumar ta gargadi ɗalibai da masu kula da cibiyoyin jarabawa da su guji saba ƙa’idoji, tana mai jaddada cewa za a ɗauki matakan ladabtarwa masu tsauri kan duk wanda aka samu da laifi.
