News
TAFTA Ta Horar da Matasa 28,000 A Kano, Ta Samar da Aikin Yi Ga 16,000
Kano: Cibiyar Terra Academy for the Arts (TAFTA) tare da haɗin gwiwar Mastercard, ta horar da matasa 28,000 a Jihar Kano domin ƙarfafa tattalin arziki da rage rashin aikin yi a tsakanin matasa.
Manajan shirin na TAFTA a Kano, Abubakar Balarabe, ya bayyana hakan yayin taron da aka gudanar a Kano, inda ya ce shirin na da niyyar haɗa koyon sana’o’i da damar samun aikin yi ko kafa kasuwanci.
KANO: Wasu Bata Gari Sun Sarewa Wani Mai Mukamin Gargajiya Hannu Yayin Kai Dauki
Ya ce mahalarta an horas da su a fannoni kamar animation, rubutun shiri (scriptwriting), fasaha, kasuwanci, ƙirar sauti da hasken dandalin wasan kwaikwayo, inda shirin ya kasance a Kano, Lagos da Ogun.
Balarabe ya ƙara da cewa, shirin wanda yanzu ya shiga shekara ta huɗu a Kano, yana bai wa mata matasa fifiko saboda yadda suke cikin yanayi mai buƙatar tallafi, tare da fa’idar ƙarfafa su ta fuskar tattalin arziki.
Wasu daga cikin ɗaliban da suka samu horo sun bayyana jin daɗinsu. Wata ɗaliba da ta horar a ƙirar sauti ta ce shirin ya buɗe mata sabuwar dama ta kasuwanci.
Haka kuma, Fatima Saleh, wadda ta samu horo a rubutun shiri, ta ce shirin ya ƙara mata ƙwarewa wajen inganta kasuwancinta, har ma ya ba ta damar sake komawa koyon animation domin tallata kayayyakin ta ga duniya.
Shirin TAFTA na daga cikin matakan da ake ɗauka domin bai wa matasa ilimi da ƙwarewa, musamman a fannin kere-kere da fasaha, domin rage rashin aikin yi a Najeriya.
