Connect with us

News

Wasu Fusatattun Matasa Sun Ƙona Mutum Uku Har lahira A Filato ‎

Published

on

WA 1777098124643

‎A Jihar Filato da ke tsakiyar Najeriya, wasu fusatattun Matasa sun kashe mutane uku ta hanyar ƙona su da ransu, bayan zargin su da hannu a kisan wani basarake a Ƙaramar Hukumar Langtang ta Arewa.

‎Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a ranar Juma’a, kwana guda bayan da aka kai hari gidan basaraken ƙauyen Ƙwallon, mai riƙe da sarautar Ponzi Kwallak, inda aka kashe shi a daren Alhamis.

Advertisement

Ƙungiyar Injiniyoyi Ta Najeriya Ta Karrama Dangote Da Lambar Girmamawa Ta Musamman

‎Shaidu sun bayyana cewa waɗanda ake zargin sun sace babur da wayar basaraken bayan sun hallaka shi, abin da ya haddasa fushin al’ummar yankin suka shiga nemansu.

Advertisement

‎Majiyoyi sun ce an kama mutanen ne yayin da suke yunƙurin sayar da baburin da aka sace, inda daga bisani aka ce sun amsa laifin da ake zargin su da aikatawa.

‎Sai dai, duk da yunƙurin wasu mazauna yankin na miƙa su ga jami’an tsaro, wasu fusatattun matasa sun ƙwace su, tare da cinna musu wuta har lahira a kusa da Sakatariyar Ƙaramar Hukumar.

Advertisement

‎Har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, rundunar ’yan sandan jihar ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.

‎Wannan al’amari na ƙara jaddada damuwar da ake da ita kan yadda wasu jama’a ke ɗaukar doka a hannunsu, a maimakon barin hukumomin tsaro su gudanar da bincike da hukunci bisa doka.

Advertisement

 

 

Advertisement

AMINIYA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending