Connect with us

News

Ƙungiyar Injiniyoyi Ta Najeriya Ta Karrama Dangote Da Lambar Girmamawa Ta Musamman

Published

on

IMG 20260424 WA0157 1024x5332 1 768x381

Ƙungiyar Nigerian Academy of Engineering (NAE) ta bai wa fitaccen attajirin Afirka, Aliko Dangote, lambar girmamawa ta Honorary Fellow, domin yabawa gudummawar da ya bayar wajen bunƙasa masana’antu da ke amfani da fasahar injiniya a Najeriya da ma nahiyar Afirka.

An sanar da hakan ne a wani biki da aka gudanar a birnin Lagos, inda shugaban NAE, Rahamon Bello, ya bayyana cewa wannan ita ce mafi girman karramawa da ƙungiyar ke bayarwa ga waɗanda suka yi fice wajen inganta harkokin injiniya da ci gaban tattalin arziki.

Advertisement

‎Tankar Mai Ta Murkushe Adaidaita Sahu

Ya ce karramawar ta Dangote na da alaƙa da irin rawar da ya taka a fannoni kamar gina manyan masana’antu, samar da ababen more rayuwa da kuma haɓaka masana’antu, lamarin da ya taimaka wajen ƙarfafa tattalin arzikin ƙasa.

Advertisement

Bello ya ƙara da cewa ƙungiyar, wadda aka kafa a shekarar 1997, na taka rawa wajen ba da shawara ga gwamnati da kamfanoni kan batutuwan fasaha da kirkire-kirkire, tare da haɗa manyan ƙwararru a fannin injiniya daga ciki da wajen ƙasar.

Ya bayyana cewa mutum biyar kacal aka taɓa bai wa wannan lambar a cikin shekaru 29 da suka gabata, inda Dangote ya zama mutum na shida da ya samu wannan matsayi mai daraja.

Advertisement

Shugaban ya kuma bayyana Dangote Refinery a matsayin mafi girman matatar mai a Afirka, yana mai cewa alama ce ta ƙwarewar injiniya da kuma ikon Afirka na gina manyan ayyuka na zamani.

A nasa jawabin, bako mai gabatar da lacca, Mutiu Sunmonu, ya jaddada muhimmancin juriya da shugabanci nagari ga masu masana’antu, tare da kiran ƙasashe masu tasowa su inganta zuba jari da manufofin makamashi domin samun ci gaba.

Advertisement

Shi ma shugaban ARCO Group, Alfred Okoigun, ya ce ya dace a mayar da hankali kan bunƙasa fannin injiniya a matsayin ginshiƙin ci gaban ƙasa.

A nasa ɓangaren, Benedict Oramah ya yaba da gudummawar Dangote wajen samar da ayyukan yi da bunƙasa masana’antu, yayin da gwamnan Lagos, Babajide Sanwo-Olu, ta bakin wakilinsa Adekunle Olayinka, ya ce hakan na nuna cewa Afirka na da damar fafatawa a fagen kirkire-kirkire a duniya.

Advertisement

Da yake karɓar karramawar, Dangote ya bayyana injiniya a matsayin harshen ci gaba, yana mai cewa duk wani gagarumin aiki da ke tallafawa tattalin arziki yana farawa ne daga tunanin injiniya.

Ya kuma yi alƙawarin ci gaba da tallafa wa matasa ta fannin horaswa, bincike da kirkire-kirkire ta hanyar haɗin gwiwa da ƙungiyar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending