Connect with us

News

Ya Kamata A Fara Tilasta Wa Matasa Samun Horon Soji A Najeriya – Ihejirika

Published

on

IMG 20241213 222518

Tsohon Shugaban Rundunar Sojin Kasa na Najeriya, Laftanal Janar Azubuike Ihejirika (ritaya), ya yi kira ga gwamnati da ta duba yiwuwar fara tilasta wa matasa samun horon soja a fadin kasar.

Janar Ihejirika ya ce, duba da yadda ƙalubalen tsaro ke ƙara ta’azzara a kasar, wajibi ne a gina sabuwar al’umma ta matasa masu kishin kasa, ladabi da kuma jajircewa, ta hanyar horon soja tun daga matakin bautar kasa (NYSC).

Advertisement

Hatsarin Mota Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 6 Tare Da Jikkata 13 A Titi

Ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a, yayin bikin cika shekaru 50 da kammala karatu na daliban Kwalejin Soja ta NDA ajin Regular Course 18, wanda aka gudanar a birnin tarayya Abuja.

“Duba da halin da ƙasar ke ciki, ina ganin lokaci ya yi da za mu fara la’akari da tilasta horon soja ga ’yan Najeriya. Za mu iya farawa da matasan da ke bautar ƙasa ta NYSC. Wannan zai taimaka wajen ƙarfafa fahimtar sadaukarwa da kishin ƙasa,” in ji shi.

Advertisement

Janar Ihejirika ya ce kwarewar da suka samu a horon soja tun farko ita ce ta gina musu rayuwa, ta sa suka zama masu ladabi da kishin kasa.

Ya kara da cewa hakan ne ya basu damar bayar da muhimmiyar gudunmawa a aikin soja da ci gaban kasa.

Advertisement

A cewarsa, duk wata ƙasa da ke son samun daidaito da ci gaba, dole ne ta gina tsarin da zai haifar da shugabanni masu kishin kasa daga tushe.

 

Advertisement

PM NEWS NIGERIAN 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending