News
Hatsarin Mota Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 6 Tare Da Jikkata 13 A Titi
Wani mummunan hatsarin mota da ya auku da safiyar Lahadi a titin Lagos–Badagry ya yi sanadin mutuwar mutum shida tare da jikkata wasu goma sha uku.
Hatsarin ya faru ne a kusa da unguwar MTN da ke gefen hanyar, lokacin da wata motar haya kirar Mazda da ke ɗauke da fasinjoji 19, ta buge wata babbar mota da ke tsaye a gefen hanya.
Kwamandan hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa (FRSC) reshen Badagry, Williams Manga, ya tabbatar da faruwar lamarin ga Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), inda ya ce hatsarin ya auku da misalin ƙarfe 5:50 na safe.
A cewarsa, direban motar ya yi gudu fiye da ƙima tare da yin shigar kuskure lokacin da yake ƙoƙarin kauce wa wata mota, amma sai ya ci karo da wata babbar mota da ke tsaye, wadda ba ta da rajista.
“Kafin ya yi aune, ya gamu da motar da ke tsaye a cikin duhu, ba tare da ya samu damar tsayawa ba,” in ji Manga.
Ya bayyana cewa mutum shida sun mutu nan take, yayin da wasu goma sha uku suka jikkata, ciki har da mace ɗaya. Dukkansu an garzaya da su Asibitin Gwamnati na Badagry, inda gawarwakin aka ajiye a dakin ajiye gawa.
Kwamandan ya ƙara da cewa tuni aka kwashe motocin zuwa ofishin ’yan sanda na Morogbo, tare da tabbatar da cewa an dawo da zirga-zirga yadda ya kamata a kan hanyar.
