News
Yawan Wanka Da Soso Yana Cutar Da Fata – Likitoci
Masana kula da lafiyar fata sun yi gargaɗi kan yawan amfani da soso wajen wanka, inda suka ce hakan na iya janyo lalacewar fata da kuma kamuwa da cututtuka, musamman ga masu amfani da sinadaran gyaran fata.
Ƙwararriyar likitar fata a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Uyo da ke jihar Akwa Ibom, Dr. Edesiri Ighorodje, ce ta bayyana hakan a tattaunawarta da Jaridar PUNCH , inda ta ce mutane da dama ba su san cewar soso yana iya zama barazana ga lafiyar fata ba idan aka yi amfani da shi fiye da kima.
Ta ce, “Soso kayan gogewa ne da ke cire matattun ƙwayoyin fata. Amma amfani da shi fiye da sau biyu zuwa uku a sati na iya lalata kariyar da fatar mutum ke da ita, wanda hakan kan janyo matsaloli kamar bushewa, kaikayi, kuraje, da kamuwa da cututtuka.”
A cewar likitar, wasu soson – musamman na roba ko loofah – idan ba a wanke su ko a busar da su bayan wanka ba, kan tara ƙwayoyin cuta masu haɗari irin su Staphylococcus, Pseudomonas, da Candida.
Ta bayyana cewa masu amfani da sinadaran fata na bleaching na fuskantar babbar barazana idan suka rika amfani da soso kullum.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
