Connect with us

Opinion

Matsalar Wuta: Najeriya Na Da Arziki, Amma Jama’a Na Rayuwa A Duhu

Published

on

TCN Ya samar da sabbin taransfoma a Legas don ƙara inganta hasken wutar lantarki a jihar
Spread the love

DAGA TIJJANI SARKI

Duk da cewa Najeriya ta shafe fiye da ƙarni guda tana sarrafa wuta, da kuma shekaru da dama na ƙoƙarin gyara fannin, har yanzu ba a samu sauyi mai ma’ana ba. Duhu da hayaƙin janareto sun zama abokai na kullum a gidaje da ofisoshi. Sai dai tambaya ita ce: Shin gwamnati na da niyyar gaske ne ko magana kawai ake?

An fara amfani da wutar lantarki a Najeriya a shekarar 1896 a birnin Lagos. A lokacin ne aka girke karamin injin kilowatts 60 don taimakon ayyukan gwamnati. Bayan haka ne aka kafa Hukumar Wutar Lantarki ta Najeriya (ECN) a 1950, sannan aka kafa Hukumar Dam ɗin Neja a 1962.

Advertisement

Gwamnatin Kano Ta Dakatar Da Shirye-shiryen Siyasa Kai Tsaye A Gidajen Rediyo Da Talabijin

Kodayake an gina Dam ɗin Kainji wanda zai iya fitar da wutar megawatts 760, yawanci ba ya aiki da cikakken ƙarfi saboda rashin gyara da tara ƙasa a tafkin.

Matsaloli irin su rikicin siyasa da mulkin soja sun karya ƙoƙarin gina tsari mai ɗorewa.

A shekarar 1972 ne aka haɗa hukumomin ECN da NDA aka kafa NEPA — wadda ta ƙara jefa al’umma cikin duhu. Har wasu suka ce NEPA na nufin “Never Expect Power Always”.

Advertisement

An Ce Za a Gyara, Amma Har Yanzu…

A cikin shekarar 2005 ne aka rushe NEPA aka samar da PHCN. Daga nan aka ƙara raba sashen zuwa kamfanonin samar da wuta (GenCos), na rarrabawa (DisCos), da kuma kamfanin tura wuta (TCN) da ke hannun gwamnati har yanzu.

An ce keɓantawa zai kawo sauyi, amma kusan shekaru 20 kenan babu wani ci gaba mai ma’ana. Wasu daga cikin kamfanonin sun kasa samar da ingantattun ayyuka saboda ƙarancin kudi da ƙwarewa. Hakazalika, rashin sa ido daga hukumar NERC da kin aiwatar da farashin da ya dace na daga cikin dalilan da suka kawo cikas.

Advertisement

Me Ke Hana Wutar Lantarki Dorewa?

Ga wasu daga cikin dalilan:

1. Rashin Isasshen Gas: Duk da arzikin gas da Najeriya ke da shi, bututun gas yakan fuskanci satar da kuma rashin biyan kuɗi daga kamfanonin wuta.

Advertisement

2. Rikicewar Grid: An samu rugujewar tsarin wutar kasa sau 46 daga 2017 zuwa 2023. Tsoffin kayan aiki da rashin tsarin zamani na haifar da wannan matsala.

3. Cin Hanci: Rahoton SERAP na 2017 ya nuna an kashe dala biliyan 30 daga 1999 zuwa 2015, amma har yanzu ana cikin duhu.

4. Sauya Tsare-tsare Ko da yaushe: Kowace gwamnati na zuwa da sabon tsari, ba tare da ci gaba daga inda na baya ya tsaya ba.

Advertisement

5. Rashin Yarda da Tsarin Biyan Kuɗi: Rashin mitoci da amfani da kididdigar hasashe wajen cajin mutane ya sa mutane da dama ke satar wuta.

Gwamnati Na Ƙoƙari Ko A,A?

Gwamnatin Bola Tinubu ta rattaba hannu kan Dokar Wutar Lantarki ta 2023, wacce ta baiwa jihohi damar mallakar aikin samar da wuta. Jihohi kamar Lagos, Kano da Kaduna na ƙoƙarin samar da nasu hanyoyin.

Advertisement

Haka kuma ana ƙoƙarin amfani da makamashi mai tsafta ta hannun Hukumar Samar da Wuta a Kauyuka (REA). Amma har yanzu ana fama da jinkiri da ƙarancin kayan aiki.

A yau, Najeriya na iya samar da megawatts 4,000–5,000 kacal ga fiye da mutane miliyan 200. Alhali kuwa, Afirka ta Kudu da mutane kusan rabin yawanmu na da ƙarfin megawatts 58,000.

‘Yan Najeriya sun gaji da alkawura da tsare-tsare marasa aiki. Abin da suke so shi ne a ga aiki a kasa. Har sai an tabbatar da gaskiya da rikon amana, sai matsalar wutar lantarki ta ci gaba da zama kamar walƙiyar da ke ɗan haskakawa kafin ta ɓace

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *