Opinion
Kungiyar ‘Yan Asalin Kano da ke Arewa Maso Gabas Ta Yaba da Jagorancin Sanata Barau

DAGA ABBA ANWAR
Wata gamayyar kungiyoyi da ke ƙarƙashin sunan Coalition of Kano Indigenes in North East, ƙarƙashin jagorancin Dr Adamu Ahmad, ta bayyana goyon baya da godiya ga Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, bisa abin da ta kira wakilci nagari da jajircewa wajen kawo ci gaba.
Kungiyar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta fitar bayan wani taron masu ruwa da tsaki da ta gudanar a Maiduguri a ƙarshen mako.
Makarantar Fatima Shariff School Of Media And Journalism Ta Fara Daukar Dalibai Karo Na 14
Sanarwar wadda Dr Ahmad ya sanya wa hannu, ta ce, “Sanata Barau na yi mana aiki. Mun ga kokarinsa a kafafen yada labarai. Wasu daga cikinmu ma sun ziyarci Kano don ganin ayyukan da ido. Muna da yawan jama’a da dabaru, kuma lokaci ya yi da za mu goya masa baya.”
Sun ce kafa Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma da kuma shirye-shiryen ci gaba da Sanatan ke jagoranta kamar Barau Maliya Agriculture Development Programme su ne dalilan da suka sa suke marawa tafiyarsa baya.
Kungiyar wadda ta haɗa ’yan kasuwa, matasa, mata, malaman makaranta, dalibai, direbobi, da masana daga sassa daban-daban, ta ce tana zagayawa jihohin Arewa Maso Gabas domin jin ta bakin ’yan asalin Kano da ke zaune a yankin.
Sun ce suna da niyyar gina haɗin kai da wayar da kai domin karfafa shugabanci nagari, da kuma kafa ƙungiya mai ɗorewa wadda za ta kasance tubalin ci gaban Kano da Arewa gaba ɗaya.
A cewar Dr Ahmad, sun shirya tsaf domin kaddamar da shirye-shiryen wayar da kai a matakin ƙauyuka, da kuma ɗora al’umma kan turbar daidaito tsakaninsu da shugabanni.
Abba Anwar shi ne tsohon Kakakin Gwamnan Jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje. Za a iya tuntubarsa ta: fatimanbaba1@gmail.com