News
Makarantar Fatima Shariff School Of Media And Journalism Ta Fara Daukar Dalibai Karo Na 14
Makarantar horar da ’yan jarida ta Fatima Shariff School of Media and Journalism ta bude rajistar sabbin dalibai karo na 14, tare da gayyatar matasa da ke da sha’awar aikin jarida musamman a fannin rediyo.
Makarantar da ke unguwar Dorayi Chiranchi a Jihar Kano, kusa da Rufaidah Drinks, na daya daga cikin makarantu da suka kware wajen horar da matasa a aikin jarida, ta hanyar koyar da darussa cikin sauki da fahimta.
Dangote Ya Ware Naira Biliyan 15 Domin Ayyuka A Jami’ar Kimiyya Da Fasaha Ta Kano
A cewar wata sanarwa daga shugabancin makarantar, an bude wannan sabon zangon ne domin bai wa matasa damar samun horo na musamman a fannoni da dama da suka shafi aikin jarida.
Wasu daga cikin darussan da ake koyarwa a makarantar sun hada da:
- Computer Basic
- Production
- News and Report Writing
- Jingle/Advert
- Sound Recording and Editing
Sanarwar ta ce za a fara da karatu a aji na tsawon wata uku, sannan daga bisani a tura daliban zuwa wasu gidajen rediyo domin yin horon aiki na wata uku.
Ga masu sha’awar samun karin bayani ko yin rajista, za su iya tuntubar makarantar ta wadannan lambobi:
07019200017, 08163641564, 08033132660
Ko ta imel: fatimasharifconsultancy@gmail.com
