News
Dangote Ya Ware Naira Biliyan 15 Domin Ayyuka A Jami’ar Kimiyya Da Fasaha Ta Kano
Shugaban kamfanin Dangote Group kuma Kansilan Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote (ADUSTECH), Alhaji Aliko Dangote, ya sanar da ware Naira biliyan 15 domin gudanar da muhimman ayyuka a jami’ar da ke jihar Kano.
Dangote ya bayyana hakan ne yayin bikin yaye dalibai karo na biyar da jami’ar ta gudanar a ranar Asabar, inda ya ce wannan kudade na daga cikin wani shiri na ci gaba na tsawon shekaru biyar da jami’ar ke shiryawa domin inganta darajarta har ta kai matakin jami’o’in duniya.
‘Yan Sanda Sun Kama Dillalin Kwaya A Kano, Sun Kwace Tramadol Ta Naira Miliyan 25
Daga cikin muhimman ayyukan da za a aiwatar da kudaden sun hada da:Gina sabbin dakunan kwanan dalibai, Kafa dakunan gwaje-gwaje na sashen Injiniya, Gina katafaren dakin kwamfuta na zamani da ke da intanet na awa 24 a kullum, Gina sabon ginin Majalisar Jami’a (Senate Building).
Daukar daliban da suka fi fice a bangaren Injiniya bayan kammala NYSC don ci gaba da horar da su
Dangote ya kuma yaba da kokarin Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, kan yadda yake jajircewa wajen yakar matsalar yara marasa zuwa makaranta a jihar.
“Ina rokon al’ummar da ke da hali da su rika tallafa wa gwamnati wajen shigar da yara makaranta. Wannan matsala ba ta gwamnati kadai ba ce – dole ne mu hada kai domin cigaban kasa,” in ji shi.
A nasa jawabin, Shugaban jami’ar, Farfesa Musa Tukur Yakasai, ya ce Gwamna Yusuf ya amince da biyan Naira biliyan 2.1 domin rage bashin da ke kan jami’ar.
Haka kuma, ya bayyana cewa Dangote ya riga ya biya kudin wutar lantarki da ake bin jami’arsama da Naira miliyan 300.
