Connect with us

News

Jami’ar Dangote Za Ta Ba Da Digirin Girmamawa Ga Kwankwaso, Mangal, AMMASCO Da Sauransu

Published

on

images (3)

Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudil, Jihar Kano, ta ce za ta ba da digirin girmamawa ga wasu fitattun ’yan Najeriya sakamakon gudummawar da suka bayar wa kasa.

Shugaban jami’ar, Farfesa Musa Yakasai ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar kafin bikin yaye dalibai da za a fara ranar Laraba.

Advertisement

NDLEA Ta Kama Masu Safarar Kwayoyi Fiye da 62,000 A Najeriya 

Cikin wadanda za a ba digirin girmamawa akwai Alhaji Dahiru Mangal, Chief Author Eze, Dr. Adeniyi Raji (SAN), Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da kuma Alhaji Mustapha Ado Muhammad (AMMASCO).

Farfesa Yakasai ya ce an zaɓi mutanen ne bisa la’akari da halayensu da kuma irin ayyukan jin ƙai da suke yi a cikin al’umma.

Advertisement

Ya kara da cewa dalibai 18,000 da suka kammala karatu a cikin shekaru bakwai da suka gabata za a yaye su a lokacin bikin.

Haka kuma ya tabbatar da cewa jami’ar ta ɗauki matakan tsaro domin kare lafiyar mahalarta da dukiyoyinsu.

Advertisement

Farfesa Yakasai ya ce za a sake naɗa Alhaji Aliko Dangote a matsayin Chancellor na jami’ar a karo na biyu, yayin da Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf zai kasance baƙon musamman na jami’ar a lokacin bikin.

Ya yaba da goyon bayan da gwamnatin jihar ta bayar domin ganin an gudanar da bikin lafiya lau.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending