Connect with us

News

NDLEA Ta Kama Masu Safarar Kwayoyi Fiye da 62,000 A Najeriya 

Published

on

Wasu Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Babban Jami’in Hukumar NDLEA

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) ta bayyana cewa ta kama mutane 62,595 da ake zargi da hannu a safarar miyagun kwayoyi daga watan Janairu na shekarar 2021 zuwa Maris na 2025.

Shugaban hukumar, Birgediya Janar Buba Marwa (mai ritaya), ne ya bayyana haka a ranar Talata yayin wani taron matan gwamnonin Najeriya da aka gudanar a birnin Abuja. An shirya taron ne tare da haɗin gwiwar NDLEA da Ƙungiyar Matan Gwamnoni ta Ƙasa.

Advertisement

‎Budaddiyar Wasika Ga Shehu Adamu: Hukumar Shari’a Ta Ce Zarginka Bai Da Tushe ‎

Marwa ya ce cikin waɗanda aka kama, mutane 11,628 ne kotuna a faɗin ƙasar suka samu da laifi, aka kuma yanke musu hukunci.

Ya ƙara da cewa hukumar ta kama wasu mutane 68 da ake zargin su ne manyan ‘yan barandan kwayoyi, tare da kwace miyagun kwayoyi masu nauyin kilo miliyan 10.3.

Advertisement

Baya ga haka, NDLEA ta rushe gonakin tabar wiwi da suka kai girman hekta 1,330 a fadin Najeriya.

Ya ce sama da mutane miliyan uku da rabi (3,843,789) ne suka amfana da shirye-shiryen wayar da kan, da nufin kare su daga fadawa cikin amfani da miyagun kwayoyi.

Advertisement

Marwa ya jaddada muhimmancin haɗin gwiwa da sauran hukumomi da al’umma wajen yaki da wannan matsala da ke barazana ga matasa da marasa ƙarfi.

“Ina roƙonmu da mu ƙara jajircewa wajen fuskantar wannan matsala a cikin al’umma. Wannan taron horo wani mataki ne da zai taimaka wajen shawo kan matsalar a matakin gari da unguwa,” in ji shi.

Advertisement

 

 

Advertisement

 

DAILY NIGERIAN 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending