News
Tinubu Ya Haramta Shigo Da Duk Irin Kayan Da Ake Iya Samarwa A Kamfanonin Cikin Gida
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin haramta shigo da duk wani kaya, fasaha ko ƙwarewar da ake iya samarwa a cikin ƙasar Najeriya.
Ministan Yaɗa Labarai, Malam Mohammed Idris, ne ya bayyana haka a wata ganawa da manema labarai a Abuja, inda ya ce shugaban ƙasar ya bayar da umarnin ne yayin taron Majalisar Zartarwa ta Ƙasa da aka gudanar a kwanan nan.
Jami’ar Dangote Za Ta Ba Da Digirin Girmamawa Ga Kwankwaso, Mangal, AMMASCO Da Sauransu
Ya ce an umarci Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya, Alƙali Lateef Fagbemi (SAN), da ya gaggauta shirya takardar dokar, wacce ake kira Executive Order, domin gabatarwa shugaban ƙasa ya sanya mata hannu.
A cewarsa, sabon umarnin na nufin hana shigo da duk wani kaya daga ƙasashen waje idan har ana iya samar da shi a masana’antun cikin gida.
“Idan misali za mu iya noma siga a Najeriya, to babu wani dalili da zai sa mu rika shigo da ita daga waje. Idan ma dole sai an shigo da kaya daga waje, sai da takarda ta musamman daga gwamnati,” in ji shi.
Ministan ya bayyana cewa yawan shigo da kaya daga waje na janyo asarar kuɗaɗen shiga da kuma rage ayyukan yi ga ’yan ƙasa. Ya ce dokar za ta taimaka wajen ƙarfafa masana’antun cikin gida da kuma farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa.
Wannan mataki dai na daga cikin kudirin gwamnatin Tinubu na ganin Najeriya ta dogara da kanta wajen samar da bukatunta.
