News
Amarya Ta Kashe Mijinta Bayan Kwana Tara Da Aure A Kano
An kama wata amarya mai suna Saudat a Jihar Kano bisa zargin kashe mijinta Salisu, kwanaki tara kacal bayan da aka daura auren su.
Lamarin ya faru ne da daren Litinin a unguwar Farawa da ke karamar hukumar Kumbotso, bayan da aka daura auren a ranar Lahadi, 27 ga Afrilu, 2025.
Tinubu Ya Haramta Shigo Da Duk Irin Kayan Da Ake Iya Samarwa A Kamfanonin Cikin Gida
Rahotanni sun bayyana cewa dangin ma’auratan ne suka shirya auren, amma babu soyayya tsakanin Saudat da Salisu tun farko. Majiyoyi sun ce Salisu ya fara nuna rashin yarda da auren, amma sai da iyayensa suka shawo kansa kafin a daura auren.
Wasu mazauna yankin sun ce rikici ya barke tsakanin ma’auratan, inda ake zargin Saudat da ƙoƙarin zuba wa Salisu guba, kafin daga bisani ta daba masa wuka har lahira.
Wannan lamari ya tayar da hankali a unguwar, inda wasu matasa suka yi yunƙurin kai farmaki ga Saudat, amma jami’an tsaro sun iso cikin gaggawa suka ceci ta tare da kai ta wajen ‘yan sanda.
Rundunar ‘yan sanda ta Jihar Kano ba ta fitar da cikakken bayani kan lamarin ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.
