Connect with us

News

Pakistan Ta Kai Hari A India A Matsayin Ramuwar Gayya

Published

on

images (1)

Pakistan ta ce ta kai wani hari kan India a safiyar Asabar domin rama hare-haren da India ta kai mata a makon da ya gabata.

Gidan talabijin na kasar, PTV, ya bayyana cewa an ji karar fashewa a birnin Amritsar da ke arewacin India da kuma a lardin Jammu da ke yankin Kashmir.

Advertisement

‘Yan Sanda Sun Kama Dillalin Kwaya A Kano, Sun Kwace Tramadol Ta Naira Miliyan 25

Pakistan ta ce ta kai harin ne a wasu sansanonin soja da ke cikin India, ciki har da inda ake ajiye makaman roka a yankin Beas, da filayen jiragen sama na Pathankot da Udhampur.

Harin na dauke da sunan “Operation Bunyanun Marsoos”.

Advertisement

Rikicin ya fara ne tun ranar Laraba, bayan India ta kai hari cikin Pakistan bisa zargin cewa akwai sansanonin ‘yan ta’adda da ke da hannu a harin da aka kai kan wasu masu yawon bude ido na Hindu a watan da ya gabata.

India ba ta ce komai kai tsaye ba tukuna, sai dai hukumomin kasar sun ce za su yi bayani daga baya.

Advertisement

A nata martanin, India ta ce ta harba makamai kan sansanonin jiragen sama uku da ke Pakistan — ciki har da sansanin Nur Khan, Mureed da kuma Shorkot. Pakistan ta ce yawancin makaman an dakile su kafin su yi barna.

An kuma ji karar fashewa a biranen Srinagar, Jammu, Lahore da Peshawar — abinda ke nuna cewa rikicin na kara fadada.

Advertisement

Kamfanin Dallancin Labarai Na routers ya ruwaito cewa a  akalla mutane 48 ne suka mutu tun lokacin da rikicin ya fara.

Kungiyar G7 ta bukaci kasashen biyu da su kwantar da hankali tare da komawa teburin sulhu domin gujewa karin hasarar rayuka.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending