News
Fashewar Gas Ya Hallaka Sabbin Ma’aurata Kwana Guda Bayan Aure
Wasu sabbin ma’aurata sun mutu sakamakon fashewar wata tukunyar iskar gas da ta auku a gidansu da ke birnin Islamabad, fadar Pakistan, inda suke kwana bayan kammala bikin aurensu, a cewar hukumomin agajin gaggawa.
Lamarin ya faru ne da safiyar ranar Lahadi da misalin ƙarfe 7:00 agogon kasar, daidai da ƙarfe 2:00 na dare agogon GMT.
Iran Ta Sha Alwashin Daukar Fansa Muddin Amurka Ta Kai Mata Hari
Rahotanni sun ce baya ga ma’auratan, wasu mutane shida da suka hada da baƙin da suka halarci bikin da kuma ‘yan uwansu, sun rasa rayukansu, yayin da sama da mutane goma suka jikkata.
Shaidu sun bayyana cewa wasu daga cikin wadanda suka jikkata sun makale a karkashin ɓaraguzan ginin, inda jami’an ceto suka shafe sa’o’i suna kokarin ciro su ta amfani da kayan aikin agaji na musamman.
Hukumomin agaji sun ce binciken farko ya nuna cewa fashewar ta samo asali ne daga yoyon iskar gas da ta cika cikin gidan kafin ta tashi.
Jami’an tsaro sun ce sun fara gudanar da bincike domin gano hakikanin musabbabin lamarin tare da daukar matakan kariya don hana sake aukuwar irin wannan iftila’i a nan gaba kamar yanda BBC HAUSA ta ruwaito
