News
Iran Ta Sha Alwashin Daukar Fansa Muddin Amurka Ta Kai Mata Hari
Iran ta sha alwashin daukar fansa muddin Amurka ta kai mata hari da sun an taimakon masu zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a kasar.
Iran ta yi barazanar mayar da martani ga Isra’ila da Amurka, idan har Washington ta yi kokarin kai wa Tehran hari bisa nuna goyon bayan zanga-zangar adawa da wahalhalun rayuwa a fadin Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Kansilan Shahuci Ya Taya Gwamnan Kano Murnar Cika Shekaru 63, Ya Yaba da Jagorancinsa
Kakakin majalisar dokokin Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Al Araby cewa, duk wani harin da Amurka za ta kai, za su mayar da shi a kan sansanonin soji na kasashen biyu.
A baya dai shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana goyon bayansa ga masu zanga-zangar da suka fito kan tituna. Ya ce mai yiwuwa ne ya yi amfani da karfin soji ya kai wa kasar hari idan aka kashe masu zanga-zangar.
A cewar kungiyar kare hakkin bil’adama ta HRANA da ke Amurka, adadin mutanen da aka kashe a zanga-zangar da aka shafe makonni 2 ana yi, ya kai 116, yayin da sama da 2,600 aka kama.
An shiga rana ta hudu tun bayan katsewar intanet, kazalika ana ci gaba da gudanar da zanga-zanga a sama da biranen kasar 180.
