News
Kotu Ta Yanke Wa Wani Mutum Hukuncin Kisa Bisa Kashe Jariri A Kano
Babbar Kotun Jihar Kano, karkashin Mai Shari’a Aisha Yau, ta yanke wa Abubakar Alhaji Sabo hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda kashe jaririn da ya haifa tare da budurwarsa.
Gwamnatin Jihar Kano ta gurfanar da Abubakar Sabo a gaban kotu kan laifin kisan kai .
Wanda ake tuhuma ya haifi jaririn ba tare da aure ba , sannan ya yi yunkurin kashe shi saboda budurwar ta ƙi bin umarninsa.
An kuma same shi da laifin tada rikici ga mahaifiyar jaririn lokacin da aka same shi yana bai wa jaririn fiya-fiya.
A shari’ar, Barista Safiya Yalwati Yahaya, mai gabatar da ƙara, ta gabatar da shaidu uku, yayin da wanda ake ƙara ya kare kansa.
Bayan nazarin hujjojin bangarorin biyu, kotun ta same shi da laifin kisan jariri, ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya, sannan ta ƙara masa hukuncin shekaru uku ɗaurin gidan yari saboda haddasa rauni.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
