Connect with us

News

Gwamnatin Kaduna Ta Rufe Asibitoci Da Makarantun Koyar Da Kiwon Lafiya 20 Da Ke Aiki Ba Bisa Ka’ida Ba

Published

on

Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da rufe wasu makarantun koyar da kiwon lafiya da kuma asibitoci masu zaman kansu guda 20 da aka buɗe ba bisa ka’ida ba a sassan jihar.

Kwamishinar lafiya ta jihar, Hajiya Umma Kaltum-Ahmed, ce ta bayyana hakan a ranar Juma’a, inda ta ce an ɗauki matakin ne domin tilasta bin ƙa’idojin da suka shafi kafa da gudanar da cibiyoyin lafiya.

Advertisement

Fashewar Gas Ya Hallaka Sabbin Ma’aurata Kwana Guda Bayan Aure

Ta ce horar da ma’aikatan lafiya ta hanyoyin da aka amince da su na daga cikin muhimman sharuɗɗan da dole ne masu zaman kansu su bi, domin kare lafiyar jama’a.

A cewarta, an rufe waɗannan cibiyoyi ne a kananan hukumomin Chikun, Igabi, Kaduna ta Arewa da kuma Kaduna ta Kudu, bayan da bincike ya nuna suna aiki ba tare da cikakken izini daga hukumomi ba.

Advertisement

“Matakin zai taimaka wajen kawar da asibitoci da makarantu marasa inganci da ka iya samar da ma’aikatan lafiya marasa ƙwarewa, wanda hakan ke barazana ga rayukan al’umma,” in ji ta.

Kwamishinar ta yi kira ga iyaye da su tabbatar da sahihanci da ingancin makarantu kafin su tura ’ya’yansu karatu, domin kauce wa asara da haɗurra a nan gaba.

Advertisement

Ta kuma yabawa Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, bisa yadda take cewa yana kokarin inganta fannin lafiya da tabbatar da ingantaccen tsarin kula da lafiyar jama’a a jihar.

 

Advertisement

 

PREMIUM TIMES

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending