Connect with us

News

Ni Ba Barawon Kuɗin Gwamnati Ba Ne, Akuya Ɗaya Ce Sanadiyyar Arzikina  — Dino Melaye 

Published

on

WhatsApp Image 2026 08 14 at 17.37.08

Tsohon ɗan dattawan Najeriya, Dino Melaye, ya bayyana cewa kiwon akuya guda ɗaya ne ya zama tushen arzikin da ya samu tun yana ƙarami, yana mai cewa ba sata ko wawure kuɗin gwamnati ya samo dukiyarsa ba.

Melaye ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a shirin KaaTruths Podcast, inda ya ce ya sayi akuya ta farko ne yana da shekara 12.

Kano: Gini Ya Rufta Kan Dalibai A Makarantar Islamiyya

A cewarsa, ribar da yake samu daga sayar da ’ya’yan akuyar ta taimaka masa wajen biyan kuɗin makarantar sakandare, jarabawar WAEC da JAMB, da kuma shekaru biyu na farko na karatunsa a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.

Ya ce tun yana da shekara 18 ya fara zuba kuɗi a wasu harkokin kasuwanci a ƙasashen waje, kafin daga bisani ya fara saka hannun jari a kasuwar hada-hadar kuɗi, Eurobonds da hannayen jarin wasu manyan kamfanoni na duniya, ciki har da Apple, Microsoft, Uber da Zoom.

Melaye, wanda yana daga cikin jagororin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), ya bayyana cewa kasuwancinsa ya bunƙasa daga kiwon dabbobi zuwa zuba jari a harkokin kasuwanci na ƙasa da ƙasa.

Advertisement

Ya kuma musanta zargin cewa siyasa ce ta samo masa dukiyarsa, yana mai cewa tun bayan barin aikin gwamnati a shekarar 2019, yanayin kuɗinsa bai taɓa raguwa ba.

A cewarsa, abin da ya fara da akuya guda a lokacin ƙuruciyarsa ya zama wata hanya da ta taimaka masa wajen samun ilimi da kuma gina tushen dukiyar da yake da ita a yau.

 

 

PREMIUM TIMES 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending