News
Gini Ya Rufta Kan Uwa Da ’Ya’yanta 2 AKaduna
Wata mata mai shekaru 35 da ’ya’yanta maza biyu, sun rasu bayan wani gini da ake ginawa ya rufta kan gidansu a yankin Rigasa da ke Jihar Kaduna.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 3:30 na daren ranar Juma’a a Dan Mani, Abuja Road, Kwanar Mai Dabino, Rigasa.
Amincin Tinubu Ga Barau Kan Harkar Tsaro Da Cigaban Kasa
Mijin matar, Abubakar Abba Haruna, ya ce ba ya gida lokacin da lamarin ya faru.
Ya ce babbar ’yarsa ce ta sanar da shi cewa ginin ya rufta kan mahaifiyarsu.
Haruna ya ce ya garzaya gida, inda ya tarar da maƙwabta na ƙoƙarin ceto mutanen da ginin ya danne.
Sai dai ya ce an samu matar tasa, Takiyatu, da ’ya’yansu biyu, Salisu mai shekaru biyar da Muhammad wanda bai wuce wata uku ba, duk sun rasu.
“Abin da ya faru jarabawa ce daga Allah. Abin da ya rage mana shi ne mu yi haƙuri da addu’a,” in ji Haruna.
Mai Unguwar Abuja Road, Kwanar Mai Dabino, Sani Ayuba, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa al’ummar yankin sun shiga jimami.
Ya ce maƙwabtansu sun yi ƙoƙarin ceto waɗanda ginin ya danne, amma ba su samu nasarar ceto da rai ba.
Ayuba, ya ce an sanar da jami’an tsaro game da lamarin, sannan ya yi addu’ar Allah Ya jiƙansu da rahama.
