Connect with us

News

Amincin Tinubu Ga Barau Kan Harkar Tsaro Da Cigaban Kasa

Published

on

IMG 20260815 WA0004

Daga Abba Anwar 

A wani taron harkar tsaro da cigaban kasa na duniya da a ka gudanar kwanan nan a birnin tarayya Abuja, wanda shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya tura Sanatan Kano ta Arewa, kuma Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa ta Kasa, Barau I Jibrin, wannan wakilci na nuna karfin imani da yarda da Tinubu ke da shi ga irin hobbasar da Sanatan ke yi wajen tallafawa yaki da harkar rashin tsaro a kasa.

Shi wannan taron wanda wata kungiyar Musulmin Duniya mai suna Muslim World League ta shirya tare da kungiyar nan ta Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS), ya tattaro shugabannin addinai daban daban a ciki da wajen Najeriya. Ya hada da masana na fuskoki daban daban da kuma kungiyoyin addinai masu fada-a-ji a fadin duniyar nan.

Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Kai Ziyarar Ba Zata Asibitin Kwararru Na Best Choice Dake Kano 

Wani abin arashi kuma shine an yi wannan babban taro ne daidai lokacin da kungiyoyi da shugabannin addinai ke ta cece-ku-ce kan siyasa da alakar ta da rashin tsaro. Musamman ganin yadda babban zabe na kasa ya durfafo mu.

Magana ta gaskiya ita ce, wakiltar shugaba Tinubu da Sanata Barau ya yi a wajen wannan taron ba karamin abu yake nunawa ba, kan yadda shugaban ya gamsu da ingancin Sanatan wajen hada hannu da masu ruwa da tsaki da Sanatan ke yi tuntuni, wajen ganin an magance matsalar rashin tsaro da yake addabar kasar nan da ma wasu bangarorin duniya. Musamman a jihohinmu arewa da wannan harkar ta fi kamari.

Advertisement

Hakan kuma ya na kara nuni da yarda da ingancin Sanatan wajen kishin kasa da kishin al’ummar sa da son ci gaban kasa da kuma cancantar sa na iya tsoma baki don neman samun mafita daga masifar rashin tsaro da a ke fama da ita. Ba ma a Najeriya kawai ba, a sassa daban daban na wannan duniya tamu.

Wani babban abu kuma shine ya kamata mai karatu ya kara gane cewa wakiltar shugaban kasa fa ba karamin abu ba ne. Musamman a manyan abubuwan da su ka shafi harkar tsaro da cigaban kasa. Lallai Sanata ka cika gwarzo mai hangen nesa. Wakiltar shugaban kasa ba wasa ba kuma ba duk kai ba!

Wannan wakilci har ila yau ya na kara nuni da yadda shugaban kasa ya amince da Sanata Barau wajen jibintar al’amura masu santsi da sulbi da kuma cukurkudewa dan nemo bakin zaren magance matsalolin. Wannan ba karamin sitamfin aminci da yarda da riritawa ba ne ga wannan Sanatan daga fadar shugaban kasa!

Wani abin ban sha’awa kuma shine yadda Sanatan ya makalo harkar tsaro da cigaban kasa, da shirin nan na “Renewed Hope Agenda” na gwamnatin shugaba Tinubu. Hakan na nuni da cewa Sanata ya fahimci manufofin gwamnatin Tinubu. Kuma ya san yadda zai tallata su ga al’ummar kasa da ma duniya gaba daya.

Game da abinda ya shafi harkar diflomasiyya ta tsakanin kasa da kasa kuma, za mu iya cewa tabbas shugaban kasa ya amince Sanata Barau ya yi fice a bangaren. Domin kuwa wannan taron taro ne da ya samo asalin yin sa daga ita wannan kungiya ta duniya. Wato “Muslim World League.” Kuma fadar shugaban kasa ta amince da Sanata kan ya je ya tattauna da su da dukkan mahalarta taron kan wannan gagarumin shiri na neman zaman lafiya mai dorewa.

Kuma ma ai da dadewa shi Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan ya kasance dan kasa na duniya gaba daya. Wanda a ke kira da “global citizen.” Wanda jajircewar sa da kwarewar sa su ka karade wannan kasa da ma tsallaken wannan kasa ta mu. Ina fata dai mai karatu mai manta da cewar wannan bawan Allan shine Mataimaki Na Daya na Majalisar Raya Tattalin Arzikin Afirka Ta Yamma, wato “ECOWAS Parliament.”

Advertisement

Shahararsa wajen dinke dukkan baraka dake faruwa tsakanin al’ummu ta fito fili ba tun yau ba. A jihar ta Kano da kasa gaba daya. Dama wannan yankin namu na Afirka. Ya yi shuhura wajen samar da kudurorin kara habaka zaman lafiya mai dorewa a majalisa. Wanda da yawan su sun zama dokoki. Wannan kyakkyawan tarihin nasa na daga cikin dalilan da shugaba Tinubu ya ga dacewarsa na wakici a wannan babban taro na duniya. Dan kishin kasa da kaunar zaman lafiya na yankan shakku!

Haka nan kuma wajen kara tabbatuwa kan jagorancin al’umma mai dorewa tun daga mazabarsa ta Kano ta Arewa zuwa ga kasancewarsa Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa ta Kasa, da yanzu kuma kasancewarsa wakilin shugaban kasa a taron duniya mai muhimmanci irin wannan, na nuni da kara habakarsa a fuskar shugabanci. Ba wai ba inke!

Kuma kasancewarsa jajirtacce ta fuskoki masu yawa, musamman kan harkar tsaro, sai ya zamana fadar shugaban kasa ta na mararin cewar ta samu mutumin da za a iya dogaro da shi a kodayaushe ba tare da tsoron jin kunya ba. Shi din bango ne madogara.

Domin ya kara tabbatar da kokarin da shugaban kasa ke yi ta fuskar lalubo bakin zaren kan harkokin tsaro, sai ya ce, shi Sanatan, a shafin sa na Facebook, lokacin da yake bayyana irin jawabin da ya yi a wajen taron, sai ya ce, “Na kara tabbatar musu da hobbasar da shugaban kasa ke yi dan samar da tsaro mai dorewa a wannan kasa ta mu.

Shugaban kasar nan fa ya na iya kokarin sa kuma a tsaye yake wajen ganin an ci gaba da samun cigaba mai dorewa a dukkan bangarori.”

A matsayin sa na shugaba da ya fahimci me a ke nufi da diflomasiyya ya gayawa mahalarta babban taron cewa, “A madadin shugaban kasa ina yabawa da wannan gagarumin aikin da wannan kungiya mai suna Muslim World League da ta zabi kungiyar JIBWIS wajen gudanar da wannan taro da zabar Najeriya ta zama wajen yin wannan babban taro na kasa-da-kasa.”

Advertisement

Ya kamata mu yi la’akari da cewa, muddin akwai shugabanni masu sanin ya kamata irin su Sanata Barau, to kuwa akwai fatan samuwar zaman lafiya mai dorewa a wannan kasa tamu da kuma wannan nahiyar tamu.

Haka nan wakilcin nan da wannan Sanata ya yi na shugaban kasa, na kara haska mana kwarewar sa da jajircewar sa da kuma cancantar sa a bangaren shugabancin al’umma kan abubuwan kasa da kasar kan ta.

Saboda haka kasancewarsa a cikin al’amuran al’umma ya na kara ba da kwarin gwuiwa wajen magance matsalolin tsaro dake addabar bangarorin duniya daban daban, idan ka faro daga kasar mu ta gado. Ganin sa kawai tare da la’akari da jajircewar sa babban abin alfahari ne gare mu.

 

Anwar ya rubuta wannan daga Kano

Asabar, 15 ga watan Agusta, 2026

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending