Connect with us

News

Gwamna Zulum Ya Haramta Sayar Da Fetur A Bama Da Banki

Published

on

Babagana Umara Zulum 1

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bayar da umarnin dakatar da sayar da man fetur a dukkan gidajen mai da ke cikin karamar hukumar Bama, ciki har da manyan garuruwan Bama da Banki.

Gwamnan ya bayyana cewa wannan matakin na zuwa ne a wani bangare na kokarin gwamnatin jihar na dakile ayyukan ta’addanci da kuma hana ’yan bindiga samun damar amfani da fetur wajen aiwatar da hare-harensu.

Advertisement

‎Kungiyar ‘Yan Asalin Kano da ke Arewa Maso Gabas Ta Yaba da Jagorancin Sanata Barau

A cewar wata sanarwa da mai ba gwamnan shawara kan harkokin yada labarai, Malam Dauda Iliya, ya fitar a ranar Asabar, an cimma wannan matsaya ne bayan ganawa ta musamman da hukumomin tsaro.

“Na bayar da umarnin dakatar da sayar da man fetur a garin Bama, Banki da sauran sassan karamar hukumar Bama, nan take,” in ji Gwamna Zulum.

Advertisement

Ya kara da cewa duk wani da aka kama da karya wannan doka zai fuskanci hukunci mai tsanani kamar yadda dokokin kasa suka tanada.

Garin Bama na daya daga cikin manyan yankunan da suka fi fuskantar matsalolin tsaro a jihar Borno, kuma yana kan iyaka da kasashen Chadi da Kamaru — wanda hakan ke kara muhimmancin matakin da gwamnati ta dauka.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending