News
Gwamnonin Arewa Da Sarakunan Gargajiya Sun Amince Da Kafa ‘Yan Sandan Jihohi
Gwamnonin Arewa da Sarakunan Gargajiya sun amince da kafa rundunar ‘yan sandan jihohi domin magance matsalolin tsaro da ke kara kamari a yankin da ma Najeriya baki ɗaya.
Sun bayyana haka ne yayin taron hadin gwiwa da suka gudanar a Kaduna a ranar Asabar, wanda ya haɗa Gwamnonin Arewa da Sarakunan jihohi 19 na yankin.
Shugaban kungiyar Gwamnonin Arewa, kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ne ya rattaba hannu a sanarwar bayan taron, inda ya bayyana cewa sun amince da shirin kafa ‘yan sandan jihohi tare da kira ga Majalisar Dokoki ta Kasa da ta gaggauta samar da dokar da za ta bai wa shirin kafuwa.
Sanarwar ta ce: “Kungiyar ta jaddada goyon bayanta ga kafa ‘yan sandan jihohi, tare da bukatar a hanzarta shigar da dokar da za ta ba su damar aiki.”
Shugabannin sun kuma jaddada bukatar hadin kai ba tare da la’akari da jam’iyyun siyasa ba domin tinkarar kalubalen tsaro, kana suka yaba da kokarin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu wajen magance matsalolin tsaro da bunkasa ayyukan raya kasa a Arewacin Najeriya.
Sun ce za su kara zage damtse wajen karfafa tsaro a cikin gida da kuma samar da dandamalin sa ido a kan iyakokin jihohi, tare da hadin gwiwa da Gwamnonin Najeriya domin taimakawa hukumomin tsaro na kasa.
“Kungiyar ta yanke shawarar samar da hanyoyin shiga tsakanin jihohi don karfafa tsaro a iyakokinmu, da kuma tsarin bai daya na yaki da rashin tsaro,” in ji sanarwar.
