News
India da Pakistan Sun Cimma Yarjejeniyar Tsagaita Wuta
India da Pakistan sun amince da tsagaita wuta, bayan wasu dogayen tattaunawa da suka gudana da taimakon Amurka.
Shugaban Amurka, Donald Trump, ne ya bayyana hakan a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, inda ya ce: “Bayan doguwar tattaunawa a cikin dare, ina farin cikin sanar da cewa India da Pakistan sun amince da tsagaita wuta cikin gaggawa. Ina taya su murna bisa nuna basira da fahimta.”
Makarantar Fatima Shariff School Of Media And Journalism Ta Fara Daukar Dalibai Karo Na 14
Yarjejeniyar ta zo ne a daidai lokacin da ƙasashen biyu ke ci gaba da kai wa juna hari a yankin Kashmir, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.
Ministan Harkokin Wajen Pakistan, Ishaq Dar, ya ce Pakistan da India sun cimma matsaya ta tsagaita wuta domin kauce wa zubar da jini. Ya ce Pakistan na da burin ganin zaman lafiya da tsaro a yankin, ba tare da nuna rauni a kan ‘yancinta da martabarta ba.
Shi ma Ma’aikatar Harkokin Wajen India ta tabbatar da cewa an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta, wacce za ta fara aiki daga ranar Asabar da misalin ƙarfe 5 na yamma, agogon Istanbul.
Tun da dadewa, India da Pakistan na cikin takun-saka, musamman kan yankin Kashmir da kowannensu ke ikirarin mallaka. Wannan yarjejeniya na iya zama wata hanya ta farfado da tattaunawa da kawo sauƙin tashin hankali a tsakanin su.
-
Opinion3 days ago
Ayyuka, Bin Diddigi, Biyan Kudi, Sakamako: Dabarun Kano Da Suka Zarce Jihohi 35
-
Opinion3 days ago
Tiriliyan ₦210 na Karya: Yadda Bala Wunti Ya Warware Dukkan Rudanin da Ya Mamaye Zaman Majalisar Dattawa Kan Asusun NNPC
-
News7 days ago
An Sace Shugaban Makaranta Da Dalibai Masu Rubuta Jarabawar NECO A Kogi
