Connect with us

News

Nijar Ta Dakatar Da Fitar Da Dabbobi Zuwa Ƙetare Gabanin Sallah

Published

on

images (1)

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta dakatar da fitar da dabbobi zuwa ƙasashen waje domin dakile hauhawar farashi a kasuwannin cikin gida gabanin Sallah Layya.

Ma’aikatar Kasuwanci ta ƙasar ce ta sanar da hakan, tana mai cewa matakin zai taimaka wajen ganin an samu isassun dabbobi a kasuwa lokacin bukin Sallah Eid al-Adha da ake sa ran gudanarwa a farkon watan Yuni.

Advertisement

Gwamnonin Arewa Da Sarakunan Gargajiya Sun Amince Da Kafa ‘Yan Sandan Jihohi

Ministan Kasuwanci, Abdoulaye Seydou, ya ce an hana fitar da shanu, tumaki, awaki da rakuma zuwa waje, musamman zuwa ƙasashe makwabta irin su Najeriya da Cote d’Ivoire.

Ya ce jami’an tsaro sun samu umarnin sa ido tare da ɗaukar mataki kan duk wanda ya karya wannan doka.

Advertisement

Rahotanni sun nuna cewa ƙungiyoyin masu tada ƙayar baya a Nijar da yankin Sahel suna amfani da satar dabbobi a matsayin hanya ta samun kuɗin shiga.

 

Advertisement

Wasu daga cikin dabbobin suna sayar da su a cikin gida, wasu kuma ana fitar da su waje domin taimakawa ayyukansu.

Lamarin satar dabbobi ya sa makiyaya da dama suka bar kauyukansu, lamarin da ke haddasa ƙarancin dabbobi a kasuwa da kuma ƙaruwa a farashi.

Advertisement

Nijar na ɗaya daga cikin ƙasashen da ke yawan fitar da dabbobi zuwa kasashen waje, kuma sama da kashi 90 cikin 100 na al’ummarta Musulmai ne da ke gudanar da layya a lokacin Sallah.

 

Advertisement

 

DW

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending