Connect with us

News

Majalisar Matasan Arewa Ta Bukaci Matasa Su Guji Tada Hankali A Ya Yin  Bukukuwan Sallah 

Published

on

Hukumomi a Najeriya sun tsaurara matakan tsaro da kuma sa ido sosai a birnin Kano,

Yayin da shagulgulan bikin Sallah ke karatowa, Majalisar Matasan Arewa (Northern Youth Assembly), reshen Jihar Kano, ta bukaci matasa da daukacin al’ummar jihar da su tabbatar da zaman lafiya da fahimtar juna a wannan lokaci na musamman.

Shugaban majalisar, Suleiman Idris, ne ya fitar da wannan kiran a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Laraba, inda ya ce lokacin Sallah lokaci ne na natsuwa.

Advertisement

Saudiyya Ta Hana Ɗaukar Hoto A Manyan Guraren Ibada

“Muna taya daukacin Musulmi da mazauna Kano murnar zagayowar wannan lokaci mai albarka. Muna kuma kira da a gudanar da bukukuwan cikin kwanciyar hankali da mutunta juna,” in ji shi.

Ya ce Kano jiha ce da ake alfahari da ita wajen zaman lafiya da hadin kai, kuma wajibi ne kowa ya taka rawar gani wajen kare wannan tarihi.

Advertisement

“Mu matasa ne ginshikin zaman lafiya. Kada mu bari a yi amfani da mu wajen tayar da hankali, kafin ko bayan bikin Sallah,” in ji Suleiman Idris.

Ya kara da cewa makomar jihar Kano na hannun matasa, don haka bai kamata a zubar da mutunci da kwanciyar hankali ba saboda bukatun wasu tsirarun mutane da ke neman rikici.

Advertisement

Majalisar ta kuma yaba da yadda Gwamnatin Jihar Kano ke hada gwiwa da jami’an tsaro da shugabannin al’umma wajen tabbatar da doka da oda a fadin jihar.

Majalisar ta bukaci jama’a da su rika bayar da hadin kai ga hukumomi domin tabbatar da tsaro a kowane sashe na jihar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending