News
Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane 13 Wani Sabon Harin Da Su Ka Kai A Sokoto
Aƙalla mutum 13 ne su ka rasa rayukansu sakamakon wasu sabbin hare-haren da ake zargin ƴan bindiga ne su ka kai kan al’ummomi uku a ƙaramar hukumar Sabon Birni ta jihar Sokoto, duk da ƙoƙarin jami’an tsaro na daƙile yunƙurin mamaye wata al’umma.
Hare-haren, da suka faru tsakanin yammacin Alhamis da safiyar Juma’a, sun yi sanadin mutuwar mutum shida a ƙauyen Mazau, mutum huɗu a Turtsawa ciki har da mata biyu, sannan manoma uku aka kashe a ƙauyen Tsamaye.
YOBE: Ruwa Da Iska Mai Ƙarfi Sun Hallaka Mutum Uku Tare Da Lalata Gidaje Da Dukiyoyi A Nguru
Mazauna yankin sun bayyana cewa tun da farko ƴan bindigar sun yi yunƙurin kai hari kan Unguwan Lalle a yammacin Alhamis, amma dakarun sojoji tare da jami’an sa-kai sun fatattake su bayan musayar wuta mai tsanani da ta ɗauki sa’o’i da dama.
Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce maharan sun janye ne bayan sun gamu da ƙaƙƙarfan turjiya daga haɗin gwiwar jami’an tsaro.
“Sojoji da jami’an sa-kai sun fafata da su a wani mummunan musayar wuta da ta ɗauki sa’o’i. Mun yi imanin cewa ‘yan bindigar sun yi asara mai yawa, amma sun kwashe gawarwakinsu kamar yadda suka saba yi,” in ji shi.
Ya ce bayan sun kasa mamaye Unguwan Lalle, ‘yan bindigar sun nufi ƙauyen Mazau inda suka kashe mutum shida, kafin daga bisani su wuce Turtsawa inda suka kashe wasu mutum huɗu, ciki har da mata biyu.
Ya ƙara da cewa saurin da jami’an tsaro suka kai ɗauki ya hana maharan kashe mutane fiye da haka.
Majiyar ta kuma ce da safiyar Juma’a, ‘yan bindigar sun dawo suka yi wa manoman da ke kan hanyarsu ta zuwa gonaki kwanton bauna a ƙauyen Tsamaye, inda suka kashe mutum uku.
Wani jagoran al’umma a Sabon Birni, wanda ya tabbatar da hare-haren, ya ce wannan sabon kisan na daga cikin jerin hare-haren da ‘yan bindiga suka sake ƙaddamarwa a yankin.
Ya bayyana cewa a ranar Laraba ma, ƴan bindigar sun yi garkuwa da manoma uku a Fadaman Sabon Birni.
Da aka tuntuɓi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto, DSP Ahmad Rufa’i, ya ce har zuwa lokacin bai samu cikakken rahoto kan lamarin ba.
Ya ce ar yanzu bai samu cikakkun bayanai game da hare-haren ba. Amma zai tuntuɓi baturen ƴan sanda DPO na yankin domin samun bayanan da suka dace.
-
News3 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion6 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News3 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
