News
Saraki Zai Jagoranci Kwamitin Gyaran Jam’iyyar PDP
Tsohon shugaban majalisar dattawa, Dokta Bukola Saraki, ne zai jagoranci kwamitin da za a yi amfani da shi wajen gyara jam’iyyar PDP.
Kungiyar gwamnonin jam’iyyar ce ta naɗa Saraki a wani taro da ta gudanar a gidan Gwamnan Jihar Bauchi da ke Abuja.
Nijar Ta Dakatar Da Fitar Da Dabbobi Zuwa Ƙetare Gabanin Sallah
Saraki zai yi aiki tare da wasu gwamnoni da dattawa da suka haɗa da Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal Dare; Gwamnan Filato, Caleb Muftwang; da Gwamnan Enugu.
Sauran mambobin kwamitin sun haɗa da Sanata Seriake Dickson, Sanata Ibrahim Dankwambo da kuma tsohon Gwamnan Jihar Abia, Chif Okezie Ikpeazu.
Kwamitin zai shirya taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da aka shirya za a yi ranar 27 ga watan nan, da kuma babban taron jam’iyyar na gaba.
Advertisements
