Connect with us

News

Majalisar Tarayya Ta Fara Zama Yar Amshin Shata, Dimokuradiyya Na Fuskantar Barazana  —Bukola Saraki

Published

on

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Dr. Bukola Saraki, ya bayyana damuwarsa kan yadda matsayi da ƙarfin Majalisar Tarayya ke ci gaba da raguwa a karkashin tsarin mulki na dimokuraɗiyya a Najeriya.

Saraki ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar domin bikin Ranar Dimokuraɗiyya, inda ya ce Majalisar ta fara komawa irin matsayin inuwa, ba tare da cikakken iko da yancin kanta kamar yadda doka ta tanada ba.

Advertisement

Amurka Na Neman Nisanta Kanta Daga Aikin Gabagadin Kaiwa Iran Hari Da Isra’ila 

Ya zargi ɓangarorin zartarwa da na shari’a da hannu a yunkurin da ke gudana na rage ƙarfin Majalisar, yana mai cewa hakan na nuni da barazana kai tsaye ga dimokuraɗiyya a ƙasar.

A cewarsa, “Yadda Fadar Shugaban Ƙasa ke tsoma baki a tsarin zaɓen shugabannin Majalisar Tarayya, babbar alama ce ta matsin lamba da tsangwama da ke ƙaruwa a kullum.”

Advertisement

Saraki ya jaddada cewa Majalisa na da rawar gani a tsarin mulki, musamman wajen duba daidaiton iko da tsare gaskiya da amana. Ya ce rashin yin hakan na iya sa talakawa su rasa kwarin guiwa a tsarin mulki, har ta kai ga fitowa tituna suna zanga-zanga.

“Idan har Majalisa ta gaza cika wannan nauyi da ya rataya a wuyanta, al’umma za su daina kallonta a matsayin cibiya mai kare muradunsu. Wannan na iya jefa tsarin dimokuraɗiyya cikin barazana,” in ji shi.

Advertisement

Saraki ya buƙaci ’yan Majalisar yanzu da su tashi tsaye wajen kare martabar majalisar da ’yancinta, yana mai cewa ci gaban dimokuraɗiyya na buƙatar Majalisa mai zaman kanta wadda ba za ta ji tsoro ko kuma rikon bangaranci ba wajen gudanar da aikinta.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending