Connect with us

News

Jinkirin Kotun Koli Kan Rikicin Sarautar Kano Na Barazana Ga Zaman Lafiya — Alhaji Abdussalami Yaro

Published

on

images (1)

Wani ɗan ƙasa mai kishin jihar Kano, Alhaji Abdussalami Muhammad Yaro, ya bayyana damuwa mai zurfi dangane da jinkirin yanke hukunci a Kotun Koli kan rikicin da ke tattare da masarautar Kano, yana mai cewa hakan na iya zama barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar da ma ƙasa baki ɗaya.

Alhaji Yaro ya bayyana hakan ne cikin wata wasiƙa buɗaɗɗiya da ya aikewa Babbar Alƙalin Ƙasa, Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun, mai taken: “Roƙon Gaggawa Don Sauraron Ƙara Game da Sarautar Kano Domin Kauce Wa Rikici.”

Advertisement

Majalisar Tarayya Ta Fara Zama Yar Amshin Shata, Dimokuradiyya Na Fuskantar Barazana  —Bukola Saraki

Wasiƙar, wadda aka rubuta a ranar 12 ga Yuni, 2025, aka kuma raba wa manema labarai a ranar Alhamis a Kano, ta ƙunshi buƙatar gaggauta sanya rana domin sauraron ƙarar da ke gaban kotu game da rikicin sarautar Kano, domin, a cewar sa, jinkiri yana ƙara dagula lamarin kuma yana haifar da fargaba da rashin tabbas a zukatan al’umma.

Alhaji Yaro ya bayyana cewa, rikicin masarautar Kano ya sha bamban da na sauran masarautu irin su Gwandu, wanda ya ɗauki shekaru fiye da 20 ana shari’a ba tare da wani tasiri kai tsaye ga zaman lafiyar al’umma ba. Ya ce a Kano, dukkan masu ikirarin sarauta suna zaune ne a cikin birnin, tare da mabiya masu yawa, lamarin da ke iya haifar da rikice-rikice da za su iya fin ƙarfin hukuma.

Advertisement

“Yin watsi da wannan rikici ko kuma jinkirin yanke hukunci na iya zama kamar barin wuta a cikin busasshiyar ciyawa. Idan ba a dauki matakin gaggawa ba, ana iya gamuwa da bala’in da ba za a iya shawo kansa ba,” in ji shi.

A cewarsa, jinkiri kan yanke hukunci a kan wannan batu zai iya janyo:

Advertisement

Tashin hankali da rashin tsaro

Cikas ga ayyukan gwamnati a matakin jiha

Advertisement

Raunin tsarin shari’a da faduwar karfin amincewa da kotuna daga bangaren al’umma

Ya roƙi Mai Shari’a Kekere-Ekun da ta yi amfani da matsayin da kundin tsarin mulki ya ba ta wajen umurtar ma’aikatan Kotun Koli su dauki matakin gaggawa domin tabbatar da an sanya rana cikin gaggawa don sauraron shari’ar, kafin al’amura su rikice.

Advertisement

Alhaji Yaro ya kuma bayyana cewa ba ya amfani da kafafen sada zumunta, don haka yana fatan wasikar za ta samu karɓuwa da isowa ga hukumomi da kafafen yaɗa labarai, domin isar da wannan saƙo na gaggawa.

A ƙarshe, ya yi addu’ar samun zaman lafiya a Kano da Najeriya, yana roƙon Allah Ya azurta alkalan kotuna da hikima da basira wajen tabbatar da gaskiya da adalci, domin kauce wa rikice-rikice da ka iya tayar da ƙayar baya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending