News
Kotun Koli Ta Yi Watsi Da Karar Kalubalantar Dokar Kafa Hukumar EFCC
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Kotun Koli ta yi watsi da karar da wasu Antoni Janar na jihohi suka shigar, suna kalubalantar dokar da ta kafa Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC).
Karar, wadda Antoni Janar na jihohi 16 suka fara shigar, ta nemi a rusa hukumar yaki da cin hanci da rashawa. Duk da haka, wasu jihohi sun janye daga karar, yayin da wasu suka nemi a shiga cikin karar a matsayin masu kara.
Wike Ya Dakatar Da Sakatare Janar Na Hukumar FCDA Har Sai Baba Ta Gani
Jihohin da suka fara shigar da karar sun hada da Ondo, Edo, Oyo, Ogun, Nasarawa, Kebbi, Katsina, Sokoto, Jigawa, Enugu, Benue, Anambra, Filato, Cross-River, da Neja.
Sai dai, DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa yayin ci gaba da sauraron karar a ranar 22 ga Oktoba, jihohin Imo, Bauchi, da Osun sun shiga cikin karar a matsayin masu kara, yayin da jihohin Anambra, Ebonyi, da Adamawa suka sanar da kudurinsu na janye karar su.
