News
Jama’ar Gari Sun Kashe Masu Garkuwa Da Mutane A Kano
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Wasu da ake zargi da garkuwa da mutane a ƙauyen Danshoshiya na yankin Kwanar Ɗan Gora a Jihar Kano sun baƙunci lahira bayan da mutanen ƙauyen suka lakaɗa masu dukan tsiya.
Hukumar ’yan sandan Kano ta tabbatar da faruwar lamarin tana mai cewa mutanen garin sun kwace waɗanda ake zargin ne daga hannun jami’anta kamar yanda Jaridar AMINIYA ta ruwaito
Kotun Koli Ta Yi Watsi Da Karar Kalubalantar Dokar Kafa Hukumar EFCC
Rundunar ta ce wasu ’yan ƙato da goran da suka yi nasarar cafke ababen zargin da mutanen garin ne suka lakaɗa masu dukan kawo wuƙa.
Sai dai ta ce bayan an garzaya da waɗanda abin ya shafa zuwa asibiti ne suka ce ga garinku nan.
Advertisements
