News
Jamhuriyar Nijar Ta Miƙa Buƙatar Ficewa Daga Kotun Hukunta Manyan Laifuka Ta Duniya ICC
Gwamnatin mulkin sojin Jamhuriyar Nijar ta miƙa buƙatarta a hukumance ta ficewa daga Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya ICC.
Miƙa wannan buƙatar dai na zuwa ne watanni tara bayan Nijar da ƙawayenta — Mali da Burkina Faso — sun sanar da aniyar yin hakan.
Iran Ta Ayyana Hutun Kwanaki Uku A Tehran Domin Jana’izar Ali Khamenei
Kotun da ke da hedikwata a birnin Hague na Netherlands ta bayyana cewa ta karɓi takardar buƙatar ficewar daga Nijar a ranar 18 ga watan Yuni.
Tun a watan Satumbar bara ne Nijar wadda ke ƙarƙashin jagorancin Janar Abdourahamane Tiani ta sanar tare da Mali da Burkina Faso cewa za su fice daga kotun, yayin da suka zargi kotun da zama wata kafa ta danniya da ƙasashen yamma ke amfani da ita.
Kotun ta ce ficewar Nijar za ta fara aiki ne daga ranar 18 ga Yunin 2027, wato shekara guda bayan gabatar da sanarwar kamar yadda dokokin kotun suka tanada.
Sai dai kotun ta jaddada cewa Nijar za ta ci gaba da cika dukkan sharuɗɗa da nauye-nauyen da ke kanta a matsayin mamba har zuwa lokacin da ficewar za ta fara aiki.
A cikin sanarwar da ta fitar, kotun ta ce duk da cewa shiga ko ficewa daga yarjejeniya haƙƙi ne na kowace ƙasa ƙarƙashin dokokin ƙasa da ƙasa, tana takaicin duk wata ƙasa da ta yanke shawarar barin ƙoƙarin haɗin gwiwa na yaƙi da rashin hukunta masu aikata manyan laifuffukan ƙasa da ƙasa.
Kotun ba ta yi tsokaci kan matsayin Mali da Burkina Faso ba, duk da cewa ƙasashen uku sun sanar da ficewarsu a lokaci guda.
Kasashen Sahel ɗin na fuskantar hare-haren ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi masu alaƙa da Al-Qaeda da IS, yayin da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam ke zargin dakarunsu da aikata laifuffuka kan fararen hula.
An kafa Kotun ta ICC ce a shekarar 2002 domin gurfanar da waɗanda ake zargi da aikata manyan laifuffuka kamar na yaƙi da kisan kare dangi a lokutan da ƙasashensu suka gaza ko kuma suka ƙi hukunta su.
A halin yanzu kotun na da ƙasashe mambobi 125, yayin da ƙasashe irin su Amurka, Rasha, China da Isra’ila ba sa cikin mambobinta.
