News
Wike Ya Dakatar Da Sakatare Janar Na Hukumar FCDA Har Sai Baba Ta Gani
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT) Nyesom Wike, ya dakatar da Injiniya Shehu Hadi Ahmad, Sakatare Janar na Hukumar Raya Babban Birnin Tarayya (FCDA), har sai baba ta gani.
Lere Olayinka, Mataimaki na Musamman kan Sadarwar Jama’a da Sabbin Kafofi Labarai ga Ministan ne, ya bayyana hakan cikin wata gajeriyar sanarwa a ranar Alhamis.
A cewar Olayinka, dakatarwar Ahmad ta fara aiki nan take.
Ko da yake ba a bayyana dalilin wannan mataki ba, “an umarci Sakatare Janar da aka dakatar da ya mika mulki ga Daraktan Ayyukan Injiniya na FCDA.”
-
Opinion6 days ago
Ayyuka, Bin Diddigi, Biyan Kudi, Sakamako: Dabarun Kano Da Suka Zarce Jihohi 35
-
Opinion6 days ago
Tiriliyan ₦210 na Karya: Yadda Bala Wunti Ya Warware Dukkan Rudanin da Ya Mamaye Zaman Majalisar Dattawa Kan Asusun NNPC
-
News4 days ago
Likitan El-Rufai Ya Shiga Matsala Kan Zargin Bayar Da Rahoton Jinya Na Bogi
