News
Bukola Saraki Ya Aika Tallafi Zuwa Ga Wadanda Ambaliya Ta Shafa A Mokwa
Gidauniyar tsohon shugaban majalisar dattawa, Dr. Abubakar Bukola Saraki, ta kai ziyara Mokwa da ke jihar Neja domin jajantawa da kuma taimakawa al’ummar da ambaliya ta shafa.
Ambaliyar ruwan da ta afku a garin ta yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da raba dubban jama’a da muhallansu.
Hon. Umar Faruk Mai Dattako Ya Tallafa Wa Iyalan ’Yan Siyasar Da Suka Rasu A Gwale
Wakilan gidauniyar sun fara ne da ziyarar Unguwar Hausawa — inda ambaliyar ta fi yin barna. Gidaje da dama sun rushe, inda mutane ke rayuwa ba tare da matsuguni ba.
Tawagar ta kai ziyara sansanin ‘yan gudun hijira da kuma babban asibitin Mokwa, inda suka duba marasa lafiya da suka tsira daga ambaliyar ciki har da yara da mata masu juna biyu.
Wata mace mai ciki, Ruƙayya Audu, ta ce ta rasa ’ya’yanta biyu a lokacin da ambaliyar ta afku.
Wakilan gidauniyar sun kuma kai ziyara fadar Hakimin Mokwa, Alhaji Muhammadu Aliyu Shaaba, inda suka samu tarba daga masarauta tare da jinjina kan wannan taimako.
A cewar Babban Daraktan gidauniyar a yankin, Musa Aliyu, an kawo tallafin kuɗi ne domin rage wa jama’a radadi, sannan ya roƙi kungiyoyi da mutane su taimaka.
