News
Gwamna Abba Ya Dauki Masu Gadi 17,600 Don Bai Wa Makarantun Jihar Tsaro
Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta bayyana cewa za ta ɗauki masu gadi 17,600 domin samar da tsaro a makarantun gwamnati a faɗin jihar.
Gwamnatin ta ce za a raba sabbin ma’aikatan tsaron ne a tsakanin kananan hukumomi 44 da ke cikin jihar, inda za a tura mutum 400 a kowace ƙaramar hukuma.
Mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.
A cewar sanarwar, matakin ya biyo bayan damuwar da gwamnati ke da ita kan yadda rashin tsaro ke barazana ga rayuwar ɗalibai da malamai a makarantu.
“Mun ɗauki wannan mataki ne saboda muna da alhakin kare lafiyar ’ya’yanmu da malamai. Ba za mu bari tsoro ko rashin tsaro ya hana su samun ilimi ba,” in ji Gwamna Abba yayin wani taro da aka yi a Kano.
Masu gadin da za a ɗauka za su samu horo kafin a rarraba su zuwa makarantu, inda za su riƙa kula da shigowa da fitowar mutane, da sa ido kan duk wani abu da zai iya kawo barazana, tare da haɗa kai da hukumomin tsaro idan bukata ta taso.
.
