News
’Yan Bindiga Sun Mayar Da Kauyuka 15 A Jihar Katsina Kufai
Akalla kauyuka 15 a Ƙaramar Hukumar Dandume ta Jihar Katsina sun zama babu kowa, sakamakon ƙaruwar hare-haren ’yan bindiga da ke addabar yankin.
Mazauna yankin sun shaida wa BBC cewa hare-haren ’yan bindiga sun ƙara tsananta a ƙananan hukumomin Funtua, Dandume da Bakori, musamman a sassan kudancin jihar.
GOMBE: Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Saurayi Bisa Zargin Caka Wa Budurwarsa Wuƙa A Maƙogwaro
A Funtua, wani mazaunin garin ya ce ’yan bindiga sun kai hare-hare har cikin garin duk da kasancewar jami’an tsaro a yankin. Ya ce a wani hari da suka kai, ’yan bindigar sun shiga yankin Unity Bank, inda suka sace shanu kafin su tsere.
Haka kuma, mazauna fiye da garuruwa da kauyuka 10 a Ƙaramar Hukumar Bakori sun ce yin zirga-zirga tsakanin al’ummomin yankin ya zama abin haɗari saboda barazanar ’yan bindiga.
Wani mazauni ya ce an sace mutane biyu a yankin a makon da ya gabata, yayin da wasu mutane ke ci gaba da kasancewa a hannun ’yan bindigar.
A Dandume kuwa, wani mazauni ya ce hare-haren ’yan bindiga na faruwa kusan kullum, inda suke kashe mutane, yin garkuwa da su tare da korar manoma daga gonakinsu.
Ya ce sama da mutane 100 ne aka yi garkuwa da su cikin makonni biyu, yayin da kusan kauyuka 15 suka zama babu kowa saboda hare-haren.
Mazauna yankin sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jihar Katsina da jami’an tsaro da su ƙara ƙaimi wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma, domin ba su damar komawa gidajensu da gonakinsu cikin aminci.
