Connect with us

News

An Daure Wani Fasinja Da Salatef A Cikin Jirgin American Airlines Saboda Yana Yunkurin Tayar Da Rikici

Published

on

IMG 20260906 193926 399

Wani fasinja mai suna Arthur Lundeen, mai shekaru 67, an daure shi da salatef da igiyar roba a cikin jirgin saman American Airlines bayan ya tayar da zaune tsaye tare da nuna halin tashin hankali a yayin tafiya.

Lamarin ya faru ne a ranar 3 ga Satumba, 2026, a jirgin AA618 da ya tashi daga Dallas-Fort Worth zuwa Newark, Amurka.

Gidauniyar Yahaya Sarki Ta Tallafa Wa Mata Da Matasa 200 A Birnin Kebbi

Rahotanni sun ce Lundeen ya fara ihun kalaman batanci kafin daga bisani ya rikide zuwa tashin hankali, inda ake zargin ya kai wa wani fasinja hari tare da shake shi.

Wani tsohon jami’in tsaro da wani fasinja sun shiga tsakani domin dakile shi, inda suka yi amfani da salatef, yayin da ma’aikacin jirgin ya ba su igiyoyin roba (zip ties) domin daure hannayensa.

Saboda tsananin tashin hankalin, matukin jirgin ya karkatar da jirgin zuwa Baltimore/Washington International Airport, inda jami’an tsaro suka shiga jirgin tare da kama Lundeen.

Advertisement

An tuhumi Lundeen da kai hari a mataki na biyu da kuma tayar da zaune tsaye, yayin da FBI da sauran hukumomi ke ci gaba da binciken lamarin

 

CBS NEWS 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending