News
Gidauniyar Yahaya Sarki Ta Tallafa Wa Mata Da Matasa 200 A Birnin Kebbi
Gidauniyar Yahaya Sarki ta raba tallafin kuɗi na N20,000 ga mutane 200 da suka haɗa da mata, matasa da masu buƙata ta musamman a yankin Nasarawa II, cikin ƙaramar hukumar Birnin Kebbi ta Jihar Kebbi.
An gudanar da rabon tallafin ne a ranar Lahadi a Shiyar Sarakuna da ke Gawo Nasarawa II, Birnin Kebbi.
NUJ Kano Ta Yi Allah-wadai Da Harin Da Aka Kai Wa ’Yan Jarida
Wanda ya kafa gidauniyar kuma mai ba Gwamnan Jihar Kebbi shawara na musamman kan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, Alhaji Yahaya Sarki, ya ce shirin shi ne karo na biyu da gidauniyar ta gudanar.
Ya ce an shirya shirin ne tare da haɗin gwiwar ɗan uwansa, Babban Sakataren Ma’aikatar Muhalli ta jihar, Abubakar Ahmed.
A cewarsa, tallafin na daga cikin ƙoƙarin gidauniyar na tallafa wa shirin matar Gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Nafisa Nasir Idris, na taimaka wa masu ƙaramin ƙarfi.
Ya ce waɗanda suka amfana da tallafin sun fito ne daga iyalan Sarkin Abdullahi, matasan APC na mazabar Nasarawa II, mambobin Gidauniyar Yahaya Sarki da kuma ‘Yan Sarki Youth Forum.
Alhaji Sarki ya buƙaci waɗanda suka amfana da su yi amfani da kuɗin wajen inganta rayuwarsu, sannan ya sanar da fara wani sabon zagaye na aikin feshin maganin sauro da sauran kwari a yankin.
Ya kuma yi kira ga al’ummar Nasarawa II da ta Jihar Kebbi baki ɗaya da su ci gaba da goyon bayan gwamnatin Gwamna Nasir Idris, yana mai cewa gwamnatin ta samu nasarori a fannonin ababen more rayuwa, lafiya, ilimi da kuma ƙarfafa matasa.
A nasa jawabin, Mukaddashin Shugaban Jam’iyyar APC na jihar, Alhaji Adamu Mudi Augie, da Jakadan Ajandar Sabuwar Fata, Sambo Gwandu, sun yaba da tallafin.
Shi ma Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu na jihar, Alhaji Yakubu Ahmed Birnin Kebbi, ya bayyana tallafin a matsayin wanda ya zo a kan lokaci.
Ya yi kira ga sauran masu riƙe da mukaman siyasa a jihar da su yi koyi da irin wannan shiri ta hanyar ƙaddamar da shirye-shiryen da za su taimaka wajen rage wa al’umma wahala.
Masu jawabin sun kuma yi kira ga al’ummar yankin da su fito da yawa domin zaɓar Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Nasir Idris a zaɓen 2027.
-
News1 day ago
Jam’iyyar Labour Party Ta Yi Alkawarin Kafa Hukumar Kula Da Hayar Gidaje A Kano
-
News3 days ago
Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
-
News6 days ago
KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga
