News
Kashi 68% na masu Cutar Mashako A Najeriya Ba Su Yi Rigakafi Ba —NCDC
Hukumar Kula da Cututtuka Masu Yaɗuwa ta Najeriya (NCDC) ta ce kashi 68 cikin 100 na mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar mashaƙo (Diphtheria) a ƙasar ba su taɓa yin rigakafin cutar ba.
Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar gargaɗi da ta fitar kan ci gaba da yaɗuwar cutar a wasu sassan ƙasar, tana mai cewa ƙarancin rigakafi na ƙara wa cutar damar yaɗuwa tsakanin al’umma.
NCDC ta ce Diphtheria cuta ce mai saurin yaɗuwa kuma mai barazana ga rayuwa, wadda ake iya kamuwa da ita ta hanyar ɗigon numfashi daga mai ɗauke da cutar yayin tari, atishawa ko kusanci.
A cewar hukumar, cutar na iya haifar da kumburin makogwaro tare da toshe hanyoyin iska, lamarin da zai iya janyo wahalar numfashi da kuma mutuwa idan ba a ba da kulawar gaggawa ba.
Rahoton NCDC ya kuma nuna cewa jihohi takwas ne ke ɗauke da kusan kashi 98 cikin 100 na dukkan mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar a Najeriya, abin da ke nuna cewa cutar ta fi kamari a wasu yankuna.
Saboda haka, masana kiwon lafiya sun yi kira ga hukumomi da su ƙara yawan allurar rigakafin cutar a jihohin da abin ya fi shafa, yayin da NCDC ta buƙaci iyaye da masu kula da yara su tabbatar da cewa sun kai ‘ya’yansu cibiyoyin lafiya domin yin rigakafin cutar.
-
News1 day ago
Jam’iyyar Labour Party Ta Yi Alkawarin Kafa Hukumar Kula Da Hayar Gidaje A Kano
-
News3 days ago
Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
-
News6 days ago
KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga
