News
GOMBE: Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Saurayi Bisa Zargin Caka Wa Budurwarsa Wuƙa A Maƙogwaro
Rundunar ’Yan sandan Jihar Gombe, ta kama wani matashi, Mamuda Danladi, bisa zargin caka wa wata budurwa mai suna Martha Danladi, mai shekaru 20, wuƙa a maƙogwaro a garin Dukku.
Rahotanni sun ce an kai Martha asibiti domin samun kulawar likitoci bayan ta samu rauni.
Dan Najeriya Ya Mutu Sanadiyyar Aikin Kara Girman Mazakutarsa
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne bayan rikici ya ɓarke a tsakaninsu kan batun aure.
Ana zargin Mamuda ya taɓa yi wa Martha alƙawarin aure, amma daga baya ya ce iyayensa sun hana shi aurenta.
Bayan haka, Martha ta buƙaci ya daina shiga harkokinta, lamarin da ake zargin ya fusata matashin har ya kai mata hari da wuƙa.
’Yan sanda sun kama Mamuda kuma suna ci gaba da bincike kan lamarin.
Har yanzu ba a samu cikakken bayani kan halin da Martha ke ciki.
Hakazalika, rundunar ba ta sanar da lokacin da za ta gurfanar da shi a kotu ba, amma ta ce tana ci gaba da bincike.
-
News6 days ago
Magoya Bayan APC Sun Yi Allah-Wadai da Rushe Gidan Sani Sha’aban, Sun Buƙaci a Yi Adalci
-
News5 days ago
Ƙungiyar ’Yan Kasuwar Wayoyi Ta Buƙaci NCC Ta Dakatar Da Tsarin Tantance Wayoyi Na DMS Tsawon Kwanaki 90
-
News6 days ago
Musa Illiyasu Kwankwaso Ya Taya Sanata Lado Murnar Cika Shekaru 60, Ya Kira Shi Gogaggen Ɗan Siyasa

